DAMAN ASHE HAKA SO YAKE? 2



*💔DAMAN ASHE HAKA SO YAKE?? 💔*


_Fitowa ta 2 (cigaba)_


*LABARIN SOYAYYAR WATA YARINYA🕊️*


💔A Fitowa ta farko mun ji yadda wannan baiwar Allah ta hadu da wannan saurayi har suka saba sosai ta kai ga duk wata damuwarsa ita yake fadawa, to zamu cigaba a inda take cewa: 

💔Wasu lokutan ba ya samun damar kirana, sai mu dauki satuttuka bamuyi waya ba saboda yana da karancin kudin da zai sa kati ya kirani. Ya kan yi tafiya daga ofis zuwa gida daga gida zuwa ofishi kullun acikin zafin rana. Na san cewa ba zai karɓi kuɗi daga wurina ba ko da na ba shi. Saboda haka nake saka masa kati ta hanyar gaya masa cewa ya dinga kirana kowane rabin sa'a muna gaisawa saboda ina kewarsa sosai. Na kan yi masa kyautar riguna, takalma, agogo har da laima ma don kare zafin rana ko ruwan sama. Duk lokacin kuma da ya samu dama yazo wajena na kan dafa masa abincin da ya fi so da kaina in kawo masa ya ci ya ji daɗin abincin kuma don kada in ɗora masa nauyin zuwa gidan cin abinci. Har zama nayi na koyi yadda ake girki. Ban san lokacin ba, kuma ta yaya?, don me duk nake yin wannan ba- kuma na kasa dakatar da kaina akan duk wani abu da ya shafe si, kuma ban taɓa tunanin yaya makomata ya zata kasance ba idan babu shi, domin shi ne Masoyina na farko kuma mutum na farko da na taɓa bari ya sami kusanci da ni. 

 
💔Duk wannan abu da ake yi mahaifina bai san komai game da dangantakarmu ba sai mahaifiyata. 'Yan uwa da yawa sukan zo da maganganu na aure akai na. Ita kuma Mama takan tambaye ni cewa- "Beta, mai zai hana ki kira shi yazo gida don ya hadu da mu? Kin gani, mahaifinki yana ta shirin aurenki" amma ni kuma na kan guji maganarsu da cewa ni ban shirya yin aure yanzu ba saboda ban san yadda zanyi musu bayani ba akan matsala ta. Na kan yawan tambaye shi sau da yawa akan ya hadu da iyayena ko da sau ɗaya ne - aƙalla ko don sanar da su game da alaƙarmu mu? Amma sai ya kawar da kai daga gare ni yana cewa a'a, ba zai iya ba domin har yanzu yana bukatar lokaci domin ya shirya sosai. Na yarda da dukkan alkawuransa na cewa zai aure ni nan ba da dadewa ba, amma ba zan iya daina damuwa akan shi ba da kuma yadda makomarmu zata kasance tare ba. Nakan yi masa addu'a kullum, nakan yi addu'a akan Allah Ya ba shi nasara, ya ba shi arziki kuma ya cire masa damuwar sa. 🕊️


💔Ba da daɗewa ba kuwa ya ba ni labari mai kyau cewa zai je Amurka😃, ya sami visa. Yana buƙatar kuɗi da yawa amma tare da halin da yake ciki yanzu, da wuya ya iya sarrafa lakh ɗaya (wato ma'ana dai bashi da wannan kuɗaɗen). Saboda haka tare da izinin mahaifiyarsa, ya sayar da gidansu inda suke ciki. Ya kama hayar gida kusa da abokinsa kuma amininsa wanda ya taimaka masa sosai. Bai samu damar zuwa ziyarata ba a cikin waɗan nan kwanakin ba har a ƙarshe tafiyarsa ta matso kusa sosai. Na kasa iya hakuri da kaina zuwa in gan shi da kuma in hadu da mahaifiyarsa amma ban samu wannan damar ba. .


💔Duk da cewa ban samu damar haduwa da mahaifiyarsa ba amma na gamsu da ganinsa da nayi. Idanuna suka jike da hawaye domin wa ya san yaushe zai dawo? Ya dawowa daga Amurka ya mai da ni amaryarsa? Wanene ya sani idan zan kasance da rai a wannan lokacin ko a'a? Kuma baya ga haka na san cewa zan rasa shi zan yi kewarsa ainihin sosai. Na yi kuka a gabansa sosai ya rike hannayena. Yana ce mani: "Kada ki damu, ba zan tafi ko'ina na barki ba, ina tare da ke a ko yaushe kuma zan kasance cikin zuciyar ki. Ki Kula da kanki sosai. Ki ci abinci da kyau? Kuma idan kina da wata matsala, ki nemi" x - (wato babban abokinsa) "don ya taimaka miki, Ina son ki. Ina son ki ". Wannan shine haduwarmu dashi ta ƙarshe kafin ya tafi Amurka. 


*_💔To Mai zai faru bayan tafiyarsa Amurka??! 🤔 ku biyomu a sannu a hankali don muji ya ta kare, shin laifin waye acikin su har ya jawo mukace "Dama haka soyayya take?"_*


_🕊️•••> Zamu cigaba a fitowa ta uku.... ✍️_


✍Rubutawa: *Yar uwarku Muhazzabin*


📝Fassarawa: *Abdullah A Abdullah Abou Khadeejat Assalafeey (أنصار السنة)*


Gabatarwa:- *Abu Abdurrahman Ahmad Umar Rimi Assalafeey (Assalafeey Rimi)*


*A ZAUREN MACEN KWARAI*



*• Ga masu buqatar shiga Zauren MACEN KWARAI sai a turo da cikakkiyar sallama tare da Cikakken suna da Address ta wannan Number kamar haka:- +2348036692586 a whatsapp.*
Post a Comment (0)