GWALAGWALEN KALMOMI ZUWA GA 'YAR UWA TA MUSULMA 1

*ZAUREN MACEN KWARAI 🧕🧕*
Ke Gabatar muku da 👇👇

*💎GWALAGWALEN KALMOMI ZUWA GA ƳAR UWATA MUSULMA 01💎*

Ya ke ƴar uwata musulma,

Ki sani, ya ke ƴar uwata musulma, cewa ke sashe ce daga jikin ɗa namiji. Ke Uwa (mahaifiyya) ce, matar wani, ƴar wani, ƙanwar wani, Antin wani, kakar wasu, kuma jikar wasu. 

Manzon Allah (ﷺ) ya ce, Mata su abokan rayuwar maza ne. [Abu Dawud].

Ke memba ce ta wannan babbar al'umma ta musulunci, al'ummar da ba'a taɓa yin irin ta ga wasu mutanen ba. Babu wata al'ummar da ta ke da maza mafi girma/daraja a duniya sannan wannan alummar. Alumma ce da ta ke kan addinin gaskiya, ta ke shiryar da mutanen ta zuwa ga tafarkin tsira.

Magabatan wannan alumma, manyan mata a musulunci, su na daga cikin dalilan da ya sa wannan alumma ta samu matsayi da girma akan sauran alummu. Allah, wanda ya azurta wannan alumma da musulunci, ya samarwa da muminai mata girma da matsayi acikin sa, su ke yiwa juna nasiha akan abu mai kyau, suke hani akan mummunan aiki, suke yiwa juna nasiha da gaskiya. Allah ya ke cewa: 

*كُنتُمْ خَيْرَ أُمَّةٍ أُخْرِجَتْ لِلنَّاسِ تَأْمُرُونَ بِٱلْمَعْرُوفِ وَتَنْهَوْنَ عَنِ ٱلْمُنكَرِ وَتُؤْمِنُونَ بِٱللَّهِ*

Kun kasance mafi alherin al'umma wadda aka fitar ga mutane kuna umurni da alheri kuma kuna hani daga abin da ake ƙi, kuma kuna ĩmani da Allah. [Suratul Al-imaran: ayata 110].

A wata ayar kuma..

*وَٱلْمُؤْمِنُونَ وَٱلْمُؤْمِنَٰتُ بَعْضُهُمْ أَوْلِيَآءُ بَعْضٍ ۚ يَأْمُرُونَ بِٱلْمَعْرُوفِ وَيَنْهَوْنَ عَنِ ٱلْمُنكَرِ وَيُقِيمُونَ ٱلصَّلَوٰةَ وَيُؤْتُونَ ٱلزَّكَوٰةَ وَيُطِيعُونَ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥٓ ۚ أُو۟لَٰٓئِكَ سَيَرْحَمُهُمُ ٱللَّهُ ۗ إِنَّ ٱللَّهَ عَزِيزٌ حَكِيمٌ*

Kuma mummunai maza da mummunai mata sashensu majiɓincin sashe ne, suna umurni da alheri kuma suna hani daga abin da ba a so, kuma suna tsayar da salla, kuma suna bayar da zakka, kuma sunaɗa ga Allah da ManzonSa. Waɗannan Allah zai yi musu rahama. Lalle Allah ne Mabuwayi, Mai hikima. [Suratul Tawbah ayata 71].

*✍Rubutawa: Abdallah A Abdallah Abu Khadijat (أنصار السنة)*
15/05/1440.
21/01/2019.


*Gabatarwa: Abu Abdurrahman Ahmad Umar Rimi Assalafeey (Assalafeey Rimi)*


*A ZAUREN MACEN KWARAI*

*· Ga masu buqatar shiga ZANREN MACEN KWARAI* *sai a turo da cikakkiyar sallama tare da cikakken suna da Address ta wannan Number +2348036692586 a whatsapp.*

Post a Comment (0)