DAMAN ASHE HAKA SO YAKE? 3


*💔DAMAN ASHE HAKA SO YAKE?? 💔*


_Fitowa ta 3 (cigaba)_


*LABARIN SOYAYYAR WATA YARINYA🕊️*


A fitowa ta 2 munji yadda Allah ya albarkace wannan saurayi da samun damar tafiya amurka, kuma har sun hadu da wannan baiwar Allah kafin tafiyarsa, take ce mana wannan itace haduwarta dashi ta ƙarshe kafin ya tafi Amurka. Yanzu zamu dora inda ta cigaba da cewa:


💔Watanni shida kenan bayan tafiyarsa amurka, ya sha wahala sosai amma ya samu nasara a rayuwarsa na siyan sabon gida, samun sabon aiki da kuma jimre wa sabon yanayin da yake ciki, amma yana kira na kuma mu kan dan yi magana amma mafi yawan lokaci na minti biyar ne. Na san cewa yana bukatar lokaci don ya huta saboda yanayin aiki da gajiya shiyasa ma bana takura masa. Ana nan haka ranaku suka tafi zuwa makonni (satittika) amma yawanci yana offline (ba'a samunsa a waya). sakonni na da kirana duk za'a bar su ba'a gani ba (unseen), koda yaushe ba'a duba su ba. Munanan tunani marasa kyau sukai ta zuwa zuciyata kullum, amma kuma nakan cigaba da gaya wa kaina cewa yana ƙaunata kuma ya damu da ni sosai, kawai dai aiki ne yayi masa yawa, kuma yana aiki ne tuƙuru saboda ni dashi kuma abubuwa za su yi dai dai nan gaba da zarar mun kasance a tare. Na kan kira "babban abokinsa sau da yawa don na tambaya game da mahaifiyarsa, yaya take da lafiyarta? Domin ita ma ita kadai ce tun lokacin da ɗanta ya tafi ƙasar waje. Yadda nake jin kewarsa a matsayin masoyiyarsa, ita ma tana ji a matsayinta na mahaifiyarsa duk da cewa tana da ƙaramin ɗanta, amma yana zaune a masaukin baki dake makaranta (hustle). Hmmm, lokacin da ya samu damar karanta sakonni na, bayan satittika da tura masa su, yakan kira ni amma bai damu da ya gaya min komai ba sai dai yace: "ayyuka ne sukai min yawa". Baya ma tambayata, yaya nake ji ba tare da shi ba?😔 .


💔Amma ni nakan gaya masa abubuwa da yawa. Na kan gaya masa cewa na je wurin shakatawa inda muka fara haduwa dashi. Nakan ce masa ina kewarsa sosai da rashinsa kusa dani da yawa. Nakan tambaye shi - shin ya yi maganar aurenmu ga mahaifiyarsa kuwa? Nakan gaya masa cewa abokin mahaifina ya nemi aurena ga dansa kuma mahaifina yana nuna sha'awa akan abun sosai. Me yakamata nayi? Ina ta kokarin kawar dakai daga maganar amma dole ne in fada masu dalilina akai? Nakan tambaye shi shin zai iya bayar da koda mintina 10 ne kawai don ya tattauna da iyayena? Nakan ci gaba da yi masa magana akan wadan nan abubuwan amma amsarsa gare ni Shiru ce kawai 😔


💔Na kan farka a tsakiyar darare, ina ta damuwa akan shi kuma ina tunanin ya makomarmu zata kasance?. Duk na rame nayi duhu sannan kuma na kamu da rashin lafiya. Na rame sosai nayi baƙi na canza kama kwanaki kuma suna ta shudewa. Iyayena sun damu da ni sosai, saboda haka ne ma Suka gaya min cewa: - idan ina da wani wanda nake so, to zasu kyale ni na aure shi saboda ni kaɗai ce 'yarsu kuma farin cikina shine farin cikinsu. Na tura masa da saqo tare da babban murmushi a fuskata zuciyata tana ta zumudi amma sai ya kira ni yana fadamin cewar: 


_*✍️Saboda yanayin tsawo rubutun zamu tsaya anan, a fitowa ta gaba zamu jin wace amsa ya bata? 😃. Shin tayi kuskuren bashi soyayyarta da kuma jiransa ko yaya abun yake?*_ 🕊️ 


_🕊️•••> Zamu cigaba a fitowa ta hudu.... ✍️_

✍Rubutawa: *Yar uwarku Muhazzabin*

📝Fassarawa: *Abdullah A Abdullah Abou Khadeejat Assalafeey (أنصار السنة)*
03/04/2020.


Gabatarwa: *Abu Abdurrahman Ahmad Umar Rimi Assalafeey (Assalafeey Rimi)*




*_ ZAUREN MACEN KWARAI _*



*• Ga masu buqatar shiga Zauren Macen Kwarai sai a turo da cikakkiyar sallama tare da Cikakken suna da Address ta wannan Number kamar haka:- +2348036692586 a whatsapp.*
Post a Comment (0)