ILLOLIN ZINA, LUWAƊI DA MAƊIGO 11


*11→ILLOLIN ZINA ,LUWADI DA MADIGO*

Madigo yakan hana ’ya mace zaman aure, domin duk wadda ta saba da shi, zai yi wahala ta rabu da shi, wanda wannan zai sa ta kasa wadatuwa da mijinta, sai ta rika fita tana yi, har idan Allah Ya tona asirinta, mijinta ya sake ta, saki na wulakanci, ko kuma ta nemi saki da kanta ta je ta ci gaba da madigonta. Don haka: “Maganin yaya za a yi, (shi ne) kada a fara.”

7. Mai madigo ba ta karewa da duniya lafiya, ko dai tozarta a duniya, ko kuma haduwa da mummunar cuta da bala’in da ba a warkewa, sai dai kabari!

8. Madigo dabbanci ne! Kai! Dabba ma ta fi ’yar madigo.

9. Cikin madigo akwai cin amanar Allah Mahalicci, saboda an aikata abin da Ya hana, haka kuma akwai cin amanar iyaye ko miji.

10. Haduwa da azabar Allah a Lahira, idan ba a tuba ba.

Wannan kadan ke nan daga cikin illolin da madigo yake haifar wa masu yin sa. Allah Madaukakin Sarki Ya kare mu.

Hanyoyin kare kai daga zina da luwadi da madigo:

Saboda hikimar Ubangiji da rahamarSa, duk abin da Ya haramta wa bayi, to za a bude wata kofar da mutum zai biya bukatarsa ba tare da ya auka wa wancan abin da Allah Ya hana din ba. Wannan abu haka yake a nan ma, domin dai mun ji irin tarin illolin da suke tattare da yin zina da luwadi da madigo, to amma babu yadda namiji ko mace za su rayu ba tare da sun samu inda za su zubar da sha’awarsu idan ta taso ba, saboda haka sai Musulunci ya halatta wadannan abubuwa masu zuwa don kauce wa aukawa cikin zina:

1. Aure:Allah Madaukakin Sarki Ya halatta wa maza su auri mata, inda yake cewa: “Ku auri abin da kuke so na mata, bibbiyu (ko) uku-uku (ko) hurhudu. Idan kuwa kuna tsoron ba za ku iya adalci ba, to ku auri daya, ko kuma abin da damarku ta mallaka. Wannan shi ne abin da zai sa ba za ku karkace ba.” (Nisa’i: 3).

Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) kuma yana cewa, “Ya ku taron samari! Duk wanda ya samu iko (ma’ana zai iya rike mace) to ya yi aure, domin shi ne mafi kyan abin da yake sa runtse ido, kuma mafi sa a tsare farji. Duk kuwa wanda bai samu iko ba, to ya yi azumi, domin (shi azumi) kariya ne a gare shi.” Buhari da Muslim.

Wannan aya da Hadisi suna nuna mana halaccin mutum ya yi aure, kuma ya auri matar da yake so, wadda ta kwanta masa a rai, matukar ba ta cikin wadanda Allah Ya haramta masa ya aura. Saboda haka da mazinata da ’yan luwadi da masu madigo za su yi tunani da sun ga yadda Musulunci ya sauwake musu hanya, ta hanyar su yi aure, sai ya zamo duk abin da za su yi halal ne, in ma sun yi niyya Allah Ya ba su lada, kamar yadda Hadisi ya nuna.


Zamu kwana a nan, a dakacemu 

Rubutawa:- Dr, Muhammad Rabi’u Umar Rijiyar Lemo, 

Daga
*MIFTAHUL ILMI*

 ```Ga masu sha'awar Shiga Zauren MIFTAHUL ILMI WhatsApp sai a aiko da cikakken suna ta WhatsApp zuwa ga lambar Mu 07036073248```
Post a Comment (0)