MATSAYIN ZAKKA A SHARI'ANCE 8


_*⚖️MATSAYIN ZAKKA A' SHARI'ANCE⚖️*_(8)

DUKIYAR DA AKE FITAR WA ZAKKA:
DA KUMA FITATTUN DUKIYOYIN ZAKKA:

 Dukiyoyin da ake fitar wa da Zakka kashi biyu ne: 
Akwai wadanda suke fitattu ne, 
watau an san su. 
Ko dai saboda su ake yawan fada a bayanin Zakka; 
ba a fadar nau’o’in da ke cikin su. 
Ko kuma saboda su babu sabanin malamai a kan su.

 Akwai kuma wadanda ba fitattu ba. 
Ko dai saboda ba a yawan fito da su a bayani, 
ko kuma saboda malamai sun yi sabani a kan su.

FITATTUN DUKIYOYIN ZAKKA:

 Dukiyoyin da aka fi sani yayin da aka yi maganar Zakkar su ne kamar haka: Zakkar kudi, 
Zakkar dabbobi, Zakkar amfanin gona, 
Zakkar ma’adanai da binanniyar dukiyar jahiliyya da 
Zakkar dukiyar ciniki.

1. Zakkar Kudi: Asalin kudi dai, kamar yadda muka sani, su ne zinariya da azurfa. 
*(Ko dinare da dirhami)*. 
A yanzu kuwa, 
su ne kudaden da Kasashe kan bugasu, domin a dinga amfani da su a duk duniya. Ko kuma a iya Kasashen kadai.

 Kamar dai Dalar Amurka da Nairar Najeriya.

 Malamai sun hadu a kan wajibcin Zakka a kan zinariya da azurfa. Ko da kuwa ba a buga su a matsayin kudi ba. 

 Kamar a ce suna asalin siffarsu, 
ko an Kera wani mazubi da su, 
ko an yi wani abin ado da su, 
ba na mata ba. 

Za a fitar da Zakka daga zinariya 
*(watau ‘Gold’).* Idan nauyinta ya kai nauyin giram (85). Sai a fitar da kashi biyu da rabi cikin dari 2.5% 
(Wato a kasa gida arba’in(40) sai a dauki kaso daya(1) shi ne Zakkar (1/40))

 Shi kuma dinare (watau bugagge) idan ya kai dinare ashirin, sai a fitar da daya bisa hudu na dinare daya.  

Ita kuwa *Azurfa* idan nauyinta ya kai giram (595),
sai a fitar da kashi biyu da rabi cikin dari 2.5% ((Wato a kasa gida arba’in(40) sai a dauki kaso daya(1) shi ne Zakkar (1/40)).  

Shi kuma Dirhami (Watau bugagge) idan ya kai Dirhami dari biyu, 
sai a fitar da Dirhami biyar.
 Sai dai kamar yadda muka sani, 
duka biyun 
(watau Dinare da Dirhami) 
yau ba a amfani da su a matsayin kudi. Don haka abin da musulmi sukan yi a Kasashensu shi ne, sukan dauki nisabin dayansu ne su Kimanta kudin Kasarsu da shi. 

 amma zai fi dacewa a yi Kimar da Dinare (Zinariya). 
Saboda dalilai kamar haka: 

(i) Malamai sun ce Kimar Dirhami ta yi ta canzawa, daga lokaci zuwa lokaci. Ba yadda take a zamanin Annabi (SAW) ba.  

Shi kuwa Dinare bai canza ba.  
(ii) An kwatanta nisabin dinare an ga ya fi zama kusa da na dabbobi da na amfanin gona.
 (Duba FiKhuz-Zakat, juz’i na 1, sh:256 – 264).

Kenan yadda zakkar dukiya take shi ne idan dukiyar ka ta kai nisabi ko ta huce sai ka lissafata ka kasa kaso arba’in(40), 
sai ka fitar da kaso daya(1) daga ciki shine zakkar (1/40).

_*Zamuci gaba insha Allah!!*_
Rubutawa>>✍🏼
*Abubakar Salihu Kabara*

Gabatarwa_
_*ALHUSEIN ABBAN SUMAYYA*_

*_Ga masu sha'awar bin shirye shiryrnmu ta Telegram se yabi ta_*👇🏽
https://t.me/miftahul_ilmi

Dan kasancewa damu ta
WhatsApp
_*Miftahul ilmi*_
Se a turo cikakken suna da Address ta wan nan Number👇🏽
07036073248
Post a Comment (0)