DAMAN ASHE HAKA SO YAKE? 4


*💔DAMAN ASHE HAKA SO YAKE?? 💔*


_Fitowa ta 4 (cigaba)_


*LABARIN SOYAYYAR WATA YARINYA🕊️*


A fitowa ta 3 munji yadda wannan baiwar Allahn ta shiga wani irin yanayi saboda rashin masoyinta a kusa, kuma har iyayenta suka fuskanci halin da take ciki har suka amince mata akan zasu bata wanda take so, har take bamu labarin cewa ta tura masa da saqo tare da babban murmushi a fuskarta zuciyarta tana ta zumudi amma sai ya kira ta yake ce mata: 


💔“kar ki jira ni, mahaifiyata bata yarda ba kuma ni ma ba zan iya dawowa kasar nan yanzu ba. Kiyi hakuri ba zan iya auren ki ba."


💔A wannan lokacin ji nake cewa kamar dukka sama zata faɗo akan kaina😢. Sai a wannan lokacin na lura cewa duk da bayan shekaru bakwai da muka kwashe dashi, har yanzu ni bakomai bace a gare shi, wacce bai damu da ita ba da har zai iya yar da ita lokacin da ya so daga rayuwarsa. Shin hakan abu ne mai sauƙi a wajensa ya manta da komai lokaci daya? To yaya alamarina game da ni? Na yi kuka 😭 na kira shi sau da yawa. Har saqonni na dinga tura masa kamar wata mara kima ina roƙonsa kada ya guje ni kada yayi min haka amma babu abin da ya canza masa zuciyarsa. Nayi kuka har zuwa fitowan Al-Fijir, na tashi nayi addu'a ina rokon Allah da ya canza masa zuciyarsa ya dawo zuwa gare ni. Da safiya tayi mahaifiyata ta firgita sosai saboda ganin fuskata da tayi da idanuwa duk sunyi ja.


💔Mahaifina ya fuskanci halin da ake ciki. Sai ya neme ni da in kira “abokinsa” in ce masa ya zo gidanmu yana nemansa. Ya zo kuma suka tattauna da mahaifina game da matsalar abokinsa. "(mai rubutun ko wacce abin ya faru akanta ta boye sunan saurayin da na abokin shiyasa bamu ambata ba)" "abokin nasa yace wa mahaifina:-" kawuna kayi hakuri. Na yi magana da shi kuma na sami labarin cewa zai auri wata abokiyar aikinsa, wata yarinyace acan wurin da yake kuma mahaifiyarsa tana murna sosai akan abun nasu, amma bata yarda da alaqarsa da 'yar ... (wato 'yar ka ba)"
 

💔Mahaifina wanda a kowane lokaci ya kasance mai natsuwa da haquri amma sai da ya fusata ya ce: - "ya dauki 'ya ta ne a matsayin abar wasa? Kalli abinda ya yi wa 'yata! 'Yata daya tilo wacce na ke kula da ita kamar gimbiya tun bayan haihuwar ta. Menene yake tunani game da 'yata? Shin ko ta rasa wani abun ne? A kyau, a kirki (nagarta da dabi'u), a arziki Alhamdulilahi Tana da komai babu abinda ta rasa. Ta jira shi har na tsawon shekara bakwai amma shine zai yi mata sakayya da wannan sakamakon? Shin anya ma shi mutum ne kuwa?"


💔Lokacin da suke maganar, ina tsaye a wajen, tare da zuciya mai ciki da rauni. Na matso kusa da babana na sanya hannuna a tsorace a kafadansa na ce dashi - "bar shi kawai ... baba" - Ina lafiya tare da farin cikin da ya samu. Mu manta da abin da ya faru, ba zan sake yin kuka ba. "wannan itace Ranar da muka rabu. Ban sani ba ko za mu sake samun damar magana dashi ba ko yaya? . *_Amma kun san me ya faru bayan nan?_*


_*✍️To mun dai ji yadda ta kaya, kuma munji cewa harda gudunmawar mahaifiyarsa a lalacewar wannan soyayyar? Amma dai bari muji mai ya faru a gaba, shin ya dawo ko yaya, ita kuma ya rayuwarta ta kasance bayan soyayyar shekara 7 fara daga media*_ 🕊️ 


_🕊️•••> Zamu cigaba a fitowa ta biyar.... ✍️_

✍Rubutawa: *Yar uwarku Muhazzabin*

📝Fassarawa: *Abdullah A Abdullah Abou Khadeejat Assalafeey (أنصار السنة)*
03/04/2020.



Gabatarwa: *Abu Abdurrahman Ahmad Umar Rimi Assalafeey (Assalafeey Rimi)*


*- Zauren Macen Kwarai-*

*. Ga masu buqatar shiga Zauren Macen Kwarai sai a turo da cikakkiyar sallam tare da cikakken suna da Address ta wannan Number +2348036692586 a WhatsApp.*
Post a Comment (0)