_*⚖️MATSAYIN ZAKKA A' SHARI'ANCE⚖️*_(13)
ZAKKAR AMFANIN GONA:🎋🎋🎋
*malamai sun yi sabani game da sharadan Zakkar amfanin gona.*
Imamu Abu Hanifa cewa ya yi, duk abin da ake shukawa a Kasa don amfana da shi to akwai Zakka a kansa.
In ban da itatuwa da ciyayi da karmami.
Shi kuwa Imam Ahmad sai ya ce, Zakka tana wajaba ne a kan duk abin da akan auna shi kuma ya kan bushe ya dade.
Su kuwa_
Imamu Malik da Imamu Shafi’i,
sai suka ce, zakka ba ta wajaba a kan amfanin gona sai wanda ake amfani da shi a matsayin abinci, kuma za a ajiye shi ya dade bai lalace ba.
Dangane da nisabi kuwa_
shi amfanin gona nisabinsa shi ne ya kai ‘wusuKi’ biyar.
Shi ‘wusuKi’ ma’auni ne wanda kowane daya ya ke cin kwano ko tiya sittin.
Amma fa kwanon mai daidai da mudannabi hudu. Watau a taKaice dai idan aka Kiyasta abin da aka noma aka ga zai kai kwano dari uku to ya wajaba a fitar masa da Zakka.
Game da abin da za a fitar kuwa,
wannan ya danganta da irin ruwan da ya tsirar da amfanin. Idan da ruwan sama ya tsira, to sai a fitar da kashi daya cikin goma.
Idan kuwa ban ruwa aka yi, to sai a fitar da kashi daya a cikin ashirin. Saboda fadin Manzon Allah (SAW):
"فيما سقت السماء والعيون أو كان عثريا، العشر. وفيما سقي بالنضح نصف العشر".
“Abin da sama ta shayar,
ko idanun ruwa,
ko ya kasance mai jan ruwa ta jijiyarsa, to za a fitar da daya cikin goma.
Idan kuwa ban ruwa aka yi, sai a fitar da daya cikin ashirin”. (Bukhari da Muslim suka rawaito.)
Wan nan Shine Nisabin zakkar Amfanin Gona atakaice,
Wallahu A'alam
_*Zamuci gaba insha Allah!!*_
Rubutawa>>✍🏼
*Abubakar Salihu Kabara*
Gabatarwa_
_*ALHUSEIN ABBAN SUMAYYA*_
*_Ga masu sha'awar bin shirye shiryrnmu ta Telegram se yabi ta_*👇🏽
https://t.me/miftahul_ilmi
Dan kasancewa damu ta
WhatsApp
_*Miftahul ilmi*_
Se a turo cikakken suna da Address ta wan nan Number👇🏽
07036073248
