ILLOLIN ZINA, LUWAƊI DA MAƊIGO 12


*12→ILLOLIN ZINA ,LUWADI DA MADIGO*

HANYOYIN KARE KAI DAGA ZINA ,LUWADI DA MADIGO
-------------------------------chigaba

 2--Mallakar baywa Musulunci ya halatta wa namijin da ya mallaki baiwa ya yi sadaka da ita, don kare mutuncinsa da mutuncinta. Ko kuma ya ‘yanta ta ya aure ta.

3. Azumi: Yin azumi, kamar yadda hadisin da ya gabata ya nuna [wanda Bukhari da Muslim suka ruwaito] kariya ne a gare shi, saboda (shi) mai azumi, an umarce shi da ya kare gabbansa daga barin haramun, kada ya yi aikin banza, ko maganar banza, ko kallon banza, wanda kuwa duk zai yi azumi ya kiyaye gabbansa daga wadannan abubuwa, to babu ko shakka Allah zai ba shi tabbata a kan da’arsa, ba zai kyale shi ga shaidan ba, har ya kai shi zuwa ga (aikata) haramun.

4. Nisantar Abubuwan da Suke Motsa Sha’awa: Ya zama mutum yana nisantar duk wani abin da zai motsa masa sha’awarsa har ya kai shi zuwa ga neman mata, ko luwadi, ko madigo, kamar kalle-kallen finafinan batsa, karanta mujallun banza, raye-raye tsakanin maza da mata, sauraron kide-kide da sauransu. Haka nan da nisantar wuraren da ake saba wa Allah, inda yake hada maza da mata, ana shedana da ayyukan banza.

5. Shagalta da ayyukan alheri: Duk wanda zai shagaltar da kansa (wajen gudanar) da ayyukan ibada da alheri, to ba zai sami lokacin da zai je zuwa ga zina ko luwadi ko madigo ba. Musulmi na hakika, ba shi da wani lokaci da zai tafiyar da shi wajen saba wa Allah, duk lokutansa na ibada ne da tsoron Allah.

6. Tsoron Allah a koyaushe: Kamar yadda Manzon Allah (Sallallaahu Alaihi Wasallam) ya ce, “Ka ji tsoron Allah a duk inda kake”. 
kofar Tuba A Bude Take
Wani ko wata za iya tunanin cewa yanzu na ji wa’azi, to yaya zan yi in tuba in daina, kuma shin ma Allah zai karbi tuban nawa, bayan dukkan wadannan abubuwa da na aikata? Sai mu ce:
Babu wani zunubi a bayan kasa da Allah ba Ya gafarta shi, matukar dai mai yin sa ya tuba, tuba ingantacciya, saboda Allah Yana cewa, “Ka ce, ya ku bayiNa wadanda suka yi wa kansu barna kada ku debe kauna ga rahamar Allah, hakika Allah Yana gafarta zunubai gaba daya, lallai shi Allah, Mai gafara ne, Mai jinkai”. (Surar Azzumar, aya ta 53). Sannan Manzon Allah (Sallallaahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Allah Ya sanya wata kofa a wajen mafadar rana, fadinta tafiyar shekara saba’in ce, saboda tuba, ba kuma za a rufe wannan kofar ba, matukar dai rana ba ta bullo daga inda kofar take ba”. Tirmizi ne ya rawaito wannan hadisi.
A wannan aya da hadisi, za mu ga yadda Allah Madaukakin Sarki, saboda rahamarSa da falalarSa, Ya bude tangamemiyar kofar karbar tuba, har zuwa lokacin tashin alkiyama. Don haka babu wani zunubi da mutum zai yi a fadin duniyar nan, face in ya tuba, Allah zai karbi tubansa. Abin da dai ya wajaba a kiyaye yayin tuban shi ne:

• Yin nadama a kan abin da ya gabata, ya zama yana tunawa kuma yana damuwa, yana nadama, yana jin yaya ma aka yi ya aikata wannan laifin!

• kudurcewa a zuciya yayin tuba, cewa ba zai kara koma wa wannan laifi ba, har karshen rayuwarsa.
• Barin wannan sabon, in yana cikin yi ne yayin da zai tuba, kada ya ce bari in karasa, sannan sai in tuba.

• Yin tuban a lokacin da Allah Yake karba, shi ne kafin tashin alkiyama, kuma ba lokacin da yake gargarar mutuwa ba. Hakika Allah ba Ya karbar tuba a wadannan lokatai guda biyu, kamar yadda Alkur’ani da hadisi suka nuna.

• Ya zama ya sauke nauyin wani da ya hau kansa, idan kudi ne ya biya shi, in cin mutunci ne ya nemi ya yafe masa.
Wadannan su ne abubuwan da mai tuba zai kiyaye da su yayin tubarsa. Allah Madaukakin Sarki Ya sa mu dace.
Ina So In Tuba Sai Dai…
Da yawa daga cikin mutane suna son su tuba su bar zunubin da suke yi, sai wasu abubuwa sukan zo su sha gabansu, su kange su ga barin tuba din, har kuma su halaka suna kan wannan sabon, to amma mutum musulmi, wanda ya san abin da yake, ya san babu wani abin da yake kare mutum daga tuba. 

Mu kwana nan,

Rubutawa:- Dr, Muhammad Rabi’u Umar R/Lemo

Gabatarwa:- Salis kura 

Daga
*MIFTAHUL ILMI*

 ```Ga masu sha'awar Shiga Zauren MIFTAHUL ILMI WhatsApp sai a aiko da cikakken suna ta WhatsApp zuwa ga lambar Mu 07036073248```

Post a Comment (0)