ILLOLIN ZINA, LUWAƊI DA MAƊIGO 14


*14→ILLOLIN ZINA ,LUWADI DA MADIGO*
._______Rubutu na Qarshe____

Wata ta ce, ina so in tuba in bar yin zina, sai dai abokin barnata yana tsorata ni da cewa idan na ki yarda da shi, zai fallasa ni ya tona min asiri, domin kuwa yana da ‘recording’ din wasu daga cikin abubuwan da muka yi tare da shi, to yaya zan yi?

• Amsa: 
Ki sani cewa kunyar lahira ta fi ta duniya, kuma Allah Madaukakin Sarki kike saba wa ba wani dan Adam ba, Allah kuma Ya fi iko a kanki fiye da yadda wancan abokin badalarki yake da iko a kanki, Allah zai iya tona miki asiri ke da shi a nan duniya, kuma Ya ki rufa muku asiri a lahira. Don haka ki zabi kunyar duniya a kan ta lahira, ki dogara ga Allah, babu abin da zai cutar da ke nawa ne cikin mutane da suka shahara da barna da fasadi a bayan kasa, amma Allah Ya rufa musu asiri ya karbi tubansu, ya zamana ko da abokan badalarsu a baya, sun fadi wani abu a kansu, ba ya wani ta’asiri, domin dukkan zukatan bayi suna a hannun Allah ne, Yana jujjuya su yadda Ya ga dama. Don haka ki dogara ga Allah ki tuba, Allah Mai ji ne, Mai gani. Shi kuma (mai yi miki waccan barazana) ki bar shi da Allah, Zai ishar miki sharrinsa.
.
.
• Wani kuma ya ce, na yi lalata da yawa, na shigar da mutane masu dimbin yawa cikin wannan hanya, yanzu idan na tuba yaya zan yi da wadanda na rena, anya kuwa Allah Zai gafarta min?

• Amsa: 
Ka sani sanya zuciyarka ta yi wannan tunani na tuba alama ce daga cikin alamomin Allah Yana nufinka da alheri, kuma babu abin da ya wajaba a kanka face ka gaggauta tuba da barin wannan sabo, wadanda kuwa ka sanya a wannan harka ka kirawo su zuwa ga tuba, kamar yadda ka kirawo su – a baya – zuwa ga halaka, wanda duk ya amsa kana da lada, wanda kuwa ya bijere maka, to Allah Yana ji, Yana gani, kai dai ka tsarkake niyyarka ka tuba, ka yawaita istigfari da neman tsari daga wurin Allah, ka yawaita alheri, Allah Mai gafarta zunubai ne gaba daya.
.
.
• Wata kuwa cewa ta yi: Yo in ma na tuba komawa nake, sau nawa ina tuba ina komawa, don haka gara kurum in ci gaba, nan gaba na tuba!

• Amsa: 
A’a ya ’yar uwa, wannan ba dalili ba ne na kin tuba, wala’alla a baya ba ki tsarkake niyyarki ba, kina tuban ne a baki, amma zuciyarki tana tattare da abin. Kuma ki sani yawan tuba matukar da niyya mai kyau kike yi, to ko da kin koma wa laifin daga baya, wannan ba zai hana ki sake tuba ba. Don haka ki gaggauta ki sake tuba, ki kuma tsarkake niyyarki, Allah Zai taimake ki.
.
.
Wadannan kadan ke nan daga cikin irin tunanin wasu dangane da tuba. A karshe dai abin ya wajaba mu sani shi ne Allah Yana karbar tuban bayinsa gaba daya. Mai son karin bayani ya duba littafin Uridu An Atuba Walakin Na Sheikh Saleh Al-munajid, zai samu karin bayani. 
A karshe, ina rokon Allah da kyawawan sunayenSa da siffofinSa madaukaka Ya kare mu daga fadawa cikin wannan bala’i da sauran abubuwan da Ya hana, wadanda kuma aka jarraba da yi, to Allah Ya shirye su, Ya sanya su tuba su koma kan hanya madaidaiciya.
.
.
Wassalamu alaikum warahmatullaahi wabarakaatuh!

Rubutawa:- Dr, Muhammad Rabi’u Umar R/Lemo

Gabatarwa:- Salis kura 

________________________
→"Wanke hannu da ruwa Mai gudana tare da Shan ruwa akai-akai da bin dokokin Ma'aikatan lafiya na daga cikin matakan kariya daga daukar cutar corona virus kamar yadda ma'aikatan lafiya suka fada"←
_________________________
Daga
*MIFTAHUL ILMI*

 ```Ga masu sha'awar Shiga Zauren MIFTAHUL ILMI WhatsApp sai a aiko da cikakken suna ta WhatsApp zuwa ga lambar Mu 07036073248```
Post a Comment (0)