ILLOLIN ZINA, LUWAƊI DA MAƊIGO 9


*09→ILLOLIN ZINA ,LUWADI DA MADIGO*

6. Luwadi yana haifar da munanan cututtuka, irin su rashin rike bayan gida da kuraje da sanya zuciya ta yi baki wuluk da bacewar basira da kyakkyawan tunani da rashin kunya da sauransu.

7. Luwadi yana kawo kaskanci da wulakanci da tozarta, a duniya da Lahira.

8. Saduwa da mace ta dubura mummunan abu ne, wanda Ibnul kayyim – Allah Ya yi masa rahama – yake cewa, “Ba a taba halatta saduwa da mace ta dubura a harshen wani Annabi da Allah Ya aiko ba.”

9. Mai luwadi bai kai darajar dabbobi ba, saboda dabba ma ba ta haka.

10. Mai luwadi – in bai tuba ba – ba ya rabuwa da duniya lafiya, ko dai Allah Ya tozarta shi, kowa ya san aikinsa, ya wayi gari ba ya da mutunci a idon duniya gaba daya, ko kuma Allah Ya jefa masa wata mummunar cuta da zai rika fatar ya mutu kowa ya huta, saboda muninta. Allah Ya kiyashe mu.

Zamu kwana a nan, a dakacemu 

Rubutawa:- Dr, Muhammad Rabi’u Umar Rijiyar Lemo, 
Gabatarwa:- Salis kura

Don kasancewa damu a talegram sai a danna links din dake kasa 
👇
https://t.me/miftahul_ilmi

Daga
*MIFTAHUL ILMI*

 ```Ga masu sha'awar Shiga Zauren MIFTAHUL ILMI WhatsApp sai a aiko da cikakken suna ta WhatsApp zuwa ga lambar Mu 07036073248```
Post a Comment (0)