ILLOLIN ZINA, LUWAƊI DA MAƊIGO 8


*08→ILLOLIN ZINA ,LUWADI DA MADIGO*


*→Illolin luwadi a cikin al’umma:*

Ko tamtama babu cewa luwadi ya kunshi dimbin illoli da cutuwa ga mai yin sa da kuma al’ummar da yake rayuwa a cikinsu. Ga kadan daga cikinsu:

1. Luwadi yana jawo wa mai yin sa da al’umma gaba daya fushin Allah da azabarsa. Kamar yadda ya faru ga mutanen Annabi Lud (Alaihis Salam).

2. ’Yan luwadi mabarnata ne, azzalumai, mutanen banza, fasikai, haka Allah Ya siffata su a wasu ayoyi a cikin Alkur’ani Mai girma.

3. Cikin luwadi akwai almubazzaranci, saboda mai luwadi yana kashe dukiyarsa cikin abin Allah ya haramta, duk kuwa mai sanya dukiyarsa cikin haramun almubazzari ne, almubazzari kuwa dan uwan shaidan ne, kamar yadda Allah Ya fada.

4. Cikin luwadi akwai fita daga tsarin da Allah ya halicci mutum a kai, saboda Allah bai halicci namiji don ya sadu da da namiji ba. Ya halicci maza da mata ne don su ji dadi da natsuwa da juna, kamar yadda Ya fada.

5. Mai yin luwadi kazami ne, kazanta mai muni, domin ya sanya tsokarsa a cikin dubura wurin kashi da najasa.


Zamu kwana a nan, a dakacemu 

Rubutawa:- Dr, Muhammad Rabi’u Umar Rijiyar Lemo, 

Daga
*MIFTAHUL ILMI*

 ```Ga masu sha'awar Shiga Zauren MIFTAHUL ILMI WhatsApp sai a aiko da cikakken suna ta WhatsApp zuwa ga lambar Mu 07036073248```
Post a Comment (0)