ZAKKAR FIDDA KAI

Day 26
Articles 30 kan Ramadana
 
ZAKKAR KONO (FIDDA-KAI)

HUNUNCIN TA: 
Zakkar fidda-kai Wajibi ce akan dukkan Musulmi, wanda ya mallaki sa'i daya na Abinci (kamar kwano Daya kenan) wanda ya fi yawan abun da zai ciyar da iyalansa na dare da yinin Sallah. Saboda Hadisin Abdullahi dan Umar (Allah Ya kara musu yarda): “Manzon Allah (S.A.W) ya farlanta Zakkar fidda-kai a Watan Ramadana akan Mutane”. 
Bukhaariy da Muslim ne suka ruwaito shi. 
 
AKAN WA TA WAJABA? 
Zakkar fidda-kai tana wajaba ne akan Yaro Karami, da Babba, Namiji da Mace, 'Da da Bawa amma duka daga cikin Musulmi saboda Hadisin da aka karbo daga Abdullahi ɗan Umar (Allah Ya ƙara musa yarda) yace: Lallai Manzon Allah ﷺ ya wajabta yin Zakkar fidda kai ta Watan Ramadana, akan Mutane, za’a bada awon sa’i Ɗaya na Dabino ko sa'i Ɗaya na Sha’ir ko sa’i, akan kowani Ɗa ko Bawa, Babba da Ƙarami da Namiji da Mace, daga cikin Musulmai.
Muslim ya ruwaito shi.
 
Al-Imamul Khaddabiy – Allah yayi masa Rahama – yace a cikin littafin shi “Ma’alimus Sunan 3/213”: ita Zakkar wajiba ce akan ko wani mai Azumi mai wadata ko Talaka, matukar zai iya samun karfin fitarwar daga abincin shi, saboda Hadisin Abdullahi dan Abbas da a ciki yake cewa: “……… saboda tana tsarkaka Mutum daga laifuka da kuskure da yayi awatan Ramadana”. Muslim ya riwaito shi, to saboda haka ko wani mai Azumi yana da bukatar samun wannan tsarkakar……”. 
 
IRIN ABINCIN DA AKE FITARWA: 
Ana fitar da Zakkar fidda-kai gwargwadon Sa’i daya na Sha'ir kimanin Mudun Nabiyyi Hudu Kenan, ko kuma Sa’I daya na Dabino, ko kuma Sa’i daya na Alkama, saboda Hadisi ya tabbata daga Sahabi Abu Sa’eed al-khuduriy (Allah ya kara masa yarda) yace: “mun kasance muna fitar da Zakkar Kono gwargwadon Sa’i daya na Abinci da kuma Sa’i daya na Sha'ir ko Dabino akan ko wani Mutum”. 
Abu Dawuda da Imamu Ahmad suka fitar dashi.
 
Malamai sunyi sabani kan lafazin Abinci da yazo a cikin Hadisin Abu Sa'eed al-khuduriy a ciki sai ya ambaci Alkama, wasu kuwa suka ce: harda wasu ma wadanda ba Alkamar ba, amma maganar da Rai yafi natsuwa dashi shine dukkanin na'u'in abincin da ake iya aunawa, kamar Alkama da kuma sauran irin abincin muka ambata, har da Gari ma yana shiga cikin wadannan na'u'o'in, saboda duka ya faru a zamanin Annabi (S.A.W) saboda Hadisin Abdullahi dan Abbas wanda Al-Imamu Ibnu Khuzaimah ya fitar dashi da Isnadi Ingabtacce Wanda a ciki aka samu ambaton Garin, wannan magana itace tafi zama daidai In sha Allah.
Allah ya karba mana, Amin.

@AnnasihaTV


Post a Comment (0)