MATSAYIN ZAKKA A SHARI'ANCE 9


_*⚖️MATSAYIN ZAKKA A' SHARI'ANCE⚖️*_(9)

ZAKKAR DABBOBI:
 Dabbobin da ake nufi a nan su ne nau’i kala uku daga cikin dabbobin gida. 

 Watau RaKuma da shanu da waki ko tumaki. 
Zakka ba ta wajaba a kan wadan nan dabbobi sai sun cika sharadai guda hudu:

(1)-SHARADI NA DAYA: 
Sai sun kai nisabi. Watau kowane daga cikinsu yana da adadin da zai kai sannan Zakka ta hau kansa. 
Kamar yadda Hadisai suka nuna.

(2)-SHARADI NA BIYU: 
Sai sun cika shekara a wurin mai su. Domin hadisi ya nuna cewa Zakkar kudi da ta dabbobi da ta dukiyar da ake juyawa sai sun cika shekara a wurin mai su tukuna.  

Amma abin da aka haifa yana bin uwarsa ne a wannan sharadin.

(3)-SHARADI NA UKU: 
Sai sun kasance suna fita kiwo. 
Watau ba a daure su ke ba. 
Abin nufi shi ne,
idan a mafi yawan kwanakin shekara a daure suke to ba ta wajaba ba. 

Abin da ya janyo wannan sharadi shi ne Hadisin da Ahmad da Nasa’i da Abu Dawuda suka rawaito daga Bahzu bin Hakim,
daga babansa, 
wanda ya nuna haka. Da kuma wanda Bukhari ya rawaito daga Anas (RA).

 Mafi yawan malamai suna tare da wannan sharadin (watau Hanafiyya,
da Shafi’iyya,
da Hambaliyya),
in ban da Malikiyya, wadanda suke ganin ba sai dabba tana fita kowa ba. 

Sun fadi haka ne, saboda wasu hadisan ba su shardanta fita kiwo ba.

 Sauran su kuma sun bada kamar haka: 

Na farko: 
Shari’ar Musulunci tana la’akari da wahalar da mai ba da Zakka ya fuskanta wajen dora masa Zakka.

Shi ya sa ma ta bambanta wanda ya dogara da ruwan sama da wanda ya yi ban ruwa a Zakkar amfanin gona.  

To ta yaya a nan za a daidaita wanda ya ke ciyar da dabbobinsa da kudinsa da wanda ya ke sakinsu kiwo. 

Na biyu: 
Sun yi amfani da wata Ka’ida ne ta Shari’a wadda take fifita Nassi mai Kayyade Magana a kan Nassi sakakke.

 Wannan kuwa Ka’ida ce karbabbiya a wajen malaman Usulu. 
Watau fifita "MuKayyad" a kan "MudlaK”.

 SHARADI NA HUDU: Sai dabbobi sun kasance ba noma ake yi da su ba, 
kuma ba na ban ruwa ba ne, 
ba kuma na hawa ba ne, 
saboda hadisin Abu Ubaidata, daga Zuhuri, wanda ya nuna haka.

Kuma wannan shi ne ra’ayin Mazhabobi uku, ban da Malikiyya

_*Zamuci gaba insha Allah!!*_
Rubutawa>>✍🏼
*Abubakar Salihu Kabara*

Gabatarwa_
_*ALHUSEIN ABBAN SUMAYYA*_

*_Ga masu sha'awar bin shirye shiryrnmu ta Telegram se yabi ta_*👇🏽
https://t.me/miftahul_ilmi

Dan kasancewa damu ta
WhatsApp
_*Miftahul ilmi*_
Se a turo cikakken suna da Address ta wan nan Number👇🏽
07036073248
Post a Comment (0)