TAMBAYA TA 91


Tambaya
:
Shin wai idan jinin al-ada ya ɗaukewa mace kafin ketowar alfijir dole ne sai ta yi sallar magrib da Isha'i?
:
Amsa:
:
Abin da Malamai sukace akan wannan mas'ala shi ne, idan mai al'ada ta yi tsarki kafin faɗuwar rana ko kuma ta yi tsarki kafin ketowar alfijir to wajibi ne a kanta ta yi sallolin magrib da Isha'i, ko kuma azahar da la'asar, saboda tsarki yazo mata a cikin lokutan waɗannan salloli, sannan kuma zata haɗe su ne a lokaci ɗaya ta sallace su wato za tayi jam'in su ne, sai dai idan lokacin ne ya ƙure ta yadda ba zai yiwu a sallace su gaba ɗaya ba, to shikenan sai a sallaci ta ƙarshen, wannan itace fatawar da wani sashe na Sahabban Manzon Allah(ﷺ) suke bayarwa, sannan kuma mafi yawa daga cikin Malamai su ma a kan haka suka tafi, sai dai wasu daga cikin Malamai sukace iyakar sallar da ta sa mu tsarki a cikin lokacinta ne kaɗai za ta sallata:
:
Amma idan tsarki yazo mata bayan sallar asubahi ko bayan sallar azuhur ko kuma bayan sallar magrib to kawai za ta sallaci waɗannan salloli ne ɗai ɗai kun su tun da dama ba a yin jam'i a tsakanin su, 
:
To amma Malamai sun yi saɓani game da cewa idan al'ada ta zowa mace a lokacin sallah kuma ba ta riga tayi wannan sallar ba, shin wai idan ta yi tsarki dole ne sai ta rama wannan sallar ko kuwa a'a? Mazhabin Shafi'iyya da Hanabila sukace dole sai ta rama, amma Mazhabin Malikiyya da Hanafiyya sukace ba za ta rama ba tun da ba sakaci ta yi ba na kin yin sallar, kuma hakika wannan magana tafi dalilai masu Ƙarfi.
:
※(шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ)※
:
▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂
              Daga Zaυren
             Fιƙ-нυl-Iвadaт
▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂
           Mυѕтαρнα Uѕмαи
              08032531505
▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂
Doмιɴ ѕнιɢα ѕнαғιɴмυ dαкє ғαcєвooк ѕαι αѕнιɢα wαɴɴαɴ lιɴк кαwαι αyι ""lιкє""👇🏾
:
https://m.facebook.com/fiqhul.ibadat/
Post a Comment (0)