Tambaya
:
Shin wai dole ne idan Mace za tayi wankan Haila sai ta tsefe kitson da ke kanta??
:
Amsa
:
Dukkan Mālamai Fuƙaha'un da ke Mazhabobin nan guda huɗu wato:
Hanābila,
Mālikiyya,
Shāfi'iyya,
Hanafiyya,
Gabā ɗayansu sun yi Ittifāƙi akan cewa wājibi ne akan Mace ko Namiji idan yazo yin wankan tsarki ya game dukkanin jikinsa da ruwa, saboda faɗin Mαnzon Aʟʟαн(ﷺ) cewa:
:
"إن تحت كل شعرة جنابة، فاغسلوا الشعر وأنقوا البشر" (رواه أبو داود)
MA'ANA:
Lallai a ƙarƙashin kowanne gāshi (na jikin mutum) akwai janaba, danhaka ku wanke kai kuma ku tsarkake (wanke) fāta,
:
Hakanan Mālamai sunyi Ijmā'i cewa ba wajibi ba ne sai Mace ta tsēfe kitsonta idan za tayi wankan-janaba, Sai dai Mālamai sunyi Saɓani ne akan idan Mace za tayi wankan-haila, Shin dole ne sai ta tsēfe kitsonta ko kuma a'a? An samu ra'ayoyin Mālamai akan haka:
:
(1)-Ƙauli na farko shi ne, Mazhabin Mālikiyya da Shāfi'iyya sun tafi akan cewa ba wajibi ba ne sai Mace ta tsēfe kitsonta, Hujjarsu kuma sun dogara ne akan waɗansu Hadīsai da kuma Āsār na Sahabbai da a ka ruwaito,
:
(2)-Ƙauli na biyu shi ne, Mazhabin Hanābila da kuma Zāhiriyya sun tafi akan cewa wajibi ne Mace ta kwance kitsonta idan za ta yi wankan-haila, daga cikin Dalilansu sun kafa Hujja da wannan Hadisi da Mαnzon Aʟʟαн(ﷺ) Yace da A'isha:
:
"إنقضي شعرك واغتسلي" (رواه إبن ماجه)
MA'ANA:
Ki kwance gāshinki sannan kiyi wanka,
:
To Sai dai mafi yawan Mālamai sun ɗauki wannan Hadisi ne a matsayin cewa Mustahabbi ne Mace ta tsēfe kitsonta, sukace domin wannan Hadisi na A'isha acikinsa babu Hujjar cewa wajibi ne sai Mace ta tsēfe kitsonta, saboda ba wai a lokacin wankan-haila ba ne Aηηαвι(ﷺ) Yace da ita hakan ba, ya faɗi haka ne a lokacin da ta ke cikin harama da aikin hajji kuma tana cikin yin al'ada, shiyasa mafi yawa daga cikin Mālamai sun tafi ne akan cewa indai har Mace za ta zuba ruwa akanta kuma ya shiga cikin kanta sosai har ya taɓa fatar kanta, to ba dole ba ne sai ta kwance kitson da ke kanta ba, amma idan ruwan ba zai samu damar shiga cikin kanta ba in ba ta kwance ba to a nan ya zama wajibi a kanta sai ta kwance shi,
:
Danhaka dai idan an haɗa dukkan Hadīsai da kuma Āsār ɗin da sukazo akan wannan Mas'ala, sai Mālamai sukace magana mafi inganci itace Mustahabbi ne kwance kitso a wankan-haila ba wai wajibi ba ne, domin dama babban abinda ake buƙata dai shi ne ruwa ya samu shiga cikin kai sosai yadda zai iya taɓo fatar kai, shikenan wanka yayi, domin kuwa koda Mace ta tsēfe kitsonta indai ba ta zuba ruwa ya shiga cikin kantaba sosai to wankanta bai yiba, danhaka ba wai tsēfewar ake kalloba, shigar ruwa cikin gāshi ake kallo, idan yazamana ruwan ba zai shiga ba har sai in an tsēfe gāshin ne, to anan tsēfewa ta zama wajibi kenan,
:
※(шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ)※
:
▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂
Daga Zaυren
Fιƙ-нυl-Iвadaт
▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂
Mυѕтαρнα Uѕмαи
08032531505
▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂
Doмιɴ ѕнιɢα ѕнαғιɴмυ dαкє ғαcєвooк ѕαι αѕнιɢα wαɴɴαɴ lιɴк кαwαι αyι ""lιкє""👇🏾
:
https://m.facebook.com/fiqhul.ibadat/
