*⚖️TSAKANIMMU DUK DA BAMBANCIMMU//27📿*
*GINSHIQI NA 25*
*Rubutawa: Baban Manar Alqasim*
FAHIMTAR MABUBBUGAR KUSKURE
Wasu lokutan za ka iske wasu kukuran da ba zai taba yuwuwa a kawar da su gaba daya ba, saboda wani lamari dake da alaqa da asalin halitta, sai dai a dan gyara wanda zai gyaru, don in aka ce dole sai ya gyaru gaba dayannan to za a daddako wata matsalar da za a yi da-na-sanin farawar ma gaba daya, yadda ka san mace, kamar dai yadda Annabi SAW yake cewa "Mace an halicce ta ne daga qashin qirji tanqwararrennan, ba za ta taba miqe maka sambal ba a hanyar da kake so, in dai kana son ka ji dadin zama da ita to ka ji amma a tanqware take, in ka ce sai ka miqar da ita sai dai ka basge ta, basgewar kuma tana nufin sakinta (Muslim 1468).
Ibn Hajrin yake cewa: Fadin da Annabi SAW ya yi na cewa "Ku dora mata a yanyar alkhairi" kamar yana nuni ne ga cewa mata na buqatar a bi su a hankali, ba za a matsa ba bare a karya su, ba kuma za a bar su ba bare su ci gaba da zama a tanqware, sai a fahimci cewa ba za a bar mace haka a tanqware ba idan ta abka cikin abinda aka halicceta a kai na rauni da abkawa cikin sabo kai tsaye ko barin abinda ya zama wajibi a gareta, abinda ake nufi a bar ta a kan abinda ta karkata a kai na halas, a hadisin akwai maganar karkatar rai, da natsuwar zuciya, da yi mata rangwame, da haquri a kan tanqwarewarta, da nuni da cewa duk wanda ya ce sai ya miqar da ita dinnan zai rasa jin dadin rayuwa da ita"
.
Ya ce "Ga shi kuma mutum ba zai iya rayuwa ba mace ba, zai sami natsuwa a wurinta, ya buqaci taimakonta a rayuwarsa kamar dai [Annabi SAW] na cewa ne: Jindadin zama da ita ba zai yuwu ba sai da haquri (Fat'hul bari 9/954), na taba samun wani arne da ya tambaye ni mata nawa muslunci ya yarda a yi? Na san matansa biyu kuma yana mugun son amaryar, sai na ce "Kamar kai da kake da mata 2 sauranka biyu, mu har hudu aka iyakance mana" sai ya ce "Da kyau, wannan shi ne addini" ya nuna min zai bar addininsa don an matsa masa sai ya saki daya a cikinsu, ta farkon ita ce uwar 'ya'yansa ba zai iya sakinta ba, ta biyun kuma yana matuqar qaunarta, ni dai na ga mai zuciyar matan da ya bar Sunna kacokan a dalilin wasu 'yan matsalolin da ya fada shi da abokansa, tabbas da ya haqura zai iya tsallake su, haka ya tsunduma cikin son zuciya tare da saninsa cewa ya bar hanyar daidai ya koma kuskure, Allah ya yafe mana.
.
*GINSHIQI NA 26*
TSAKANIMMU DUK DA BAMBANCIMMU
Duk da bambancin da muke da shi a tsakanimmu akwai abubuwan da suka hada mu sama da wadanda suka raba mu, in dai ka dauka cewa addininnan ya fi mana kawunammu to dole ne mu taimaka masa mu nema masa kariya, mu fusata a dominsa sama da yadda muke fushi idan an yi mana wani abinda ba mu ji dadi ba, rauni ne na kishin addini a ce mutum ya fusata in aka aibanta shi ko waninsa, amma ko a jikinsa in aka tabi addinin Allah SW, ko in ma zai ce wani abu sai ka ga yana zagaye-zagaye, ka yarda da hadisan Annabi SAW, sahabbansa gaba daya, matansa ahalinsa ne, 'ya'yansa bakwai nasa ne, sunnarsa ce manhajinka, amma ka ce gwara ka zauna da wanda ya saba musu gaba daya ya zage su ma, da ka zauna da wanda bai yarda da wasu da kake ganin salihan bayi ne ba gareka, wannan kauce wa hanya ne gaskiya.
Addinin ya kamata a riqe shi a gaba kafin duk wani mutum, kar ka fadi qarara cewa: Gwara arne da wani dan uwanka musulmi, bayan kana da masaniyar cewa tabbas wanda kake fifita shi dinnan ba addininku ko aqidarku daya ba, hasali ma babban abokin gabanka ne, ka karanta ka karantar cewa ba abinda yake so kamar ka kafurta irinsa ko a rasa ka a bayan qasa gaba daya, ta ya za ka fifita shi a kan dan uwanka musulmi? Irin wannan kuskuren na qin gaskiya shi ne ya faru da Nasara, sun yarda cewa Yahudawa ne suka kashe allansu - in ya mutu kenan- wato Almasihu, musulmai kuma sun yarda da manzancinsa da littafinsa, hasali ma duk musulmin da bai yarda da annabcin Isa AS ba ba musulmi ne ba gare mu.
Muna saka wa yarammu sunansa saboda qauna kamar yadda muke saka musu sunan Muhammad, a Qur'ani ma in ka bude ga tarihansanan da saukakkiyar sura sukutum ta mahaifiyarsa da Allah SW ya tsarkake ta a ciki, amma sai Banasaren ya fi qaunar Bayahude sama da musulmi ya jibanta lamuransa gare shi, sai kuma musulmin da ya fi kusa da shi a komai ya koma abokin gabansa, Allah SW ya ce ((Ba za ka sami mutanen da suka yi imani da Allah da ranar lahira suna jibanta qauna ga wadanda suka saba wa Allah da manzonsa ba koda kuwa uwayensu ne, ko diyoyinsu, ko 'yan uwansu ko danginsu)), da abin ya yi nisa, sai yaran Nasara a yau suka dauki musulmi a matsayin abokin gabansu lamba daya, ba Yahudawan da suka yi qoqarin kashe allansu ba, ko ma suka kashe din kamar yadda koyarwar tasu take.
Mu kuma a Sunna duk mun yarda da khalifofinnan da adalcinsu, sauran sahabban mun yarda da kyakkyawar kasantuwa tare da Annabi SAW da suka yi, da jihadi tare da shi har rabuwarsu da duniya, su ne suka haddace Qur'ani a zukatansu, da hadisan Annabi SAW har suka bar duniya, amma sai ga shi wasu sun fi kusantaka da masu kafurta khalifofin, da muzanta sunan sahabban, da fasiqanta wasu daga cikin matan Annabi SAW, da qin yarda da kasancewar matan a cikin iyalin manzon, da qin yarda da 'ya'yan Annabi SAW din ma gaba daya, kai a qarshe ma duk ibadar da sunnar ta yi sai sun yi kishiyarta.
Sai gashi sun yarda su zauna da wadannan karkatattun tare a masallaci guda, su ba su damar su yi musu irin wa'azinsu, su yi sallah tare da su matuqar ba za su kira sunan waliyansu su zaga ba, an saki layi kenan, da kamata ya yi mutum ya damu matuqa idan aka tabi addininsa ba shi kansa ko wani nasa ba, ya san waye masoyinsa na qwarai waye maqiyainsa a addini, in za a zauna tare a addinance sai dai qoqarin da'awa da nuna gaskiya ko Allah zai shirye su, kuskuren an sami matsala a ma'auni, ya kamata a dauko abubuwan da suka hada mu da wadanda suka raba mu a saka a sikeli a auna sai a rinjayar da wanda ya dace.
Zamuci gaba insha Allah.
*Gabatarwa: Abulfawzhaan*
*Follow my Facebook Page*
https://www.facebook.com/100625758324355?referrer=whatsapp