ZAKKAR FIDDA KAI

*ZAKKAR FIDDA KAI!!!*
.
.
*DAGA ZAUREN*
.
*MAJALIS - SUNNAH*
.
.
مجلس السنة
📓📔
+2349032091131
+237665087032
.
.
Yau 27/ 09/ 1441 wanda yayi dai-dai da 20/ 05/ 2020.
=
=
_Godiya ta tabbata ga Allah, muna gode masa, muna neman taimakonsa, kuma muna neman tsarinsa daga sharrin kawunanmu da munanan ayyuakanmu. Hakika Wanda Allah ya shiryar Babu Mai 6atar dashi, Wanda ya 6atar Kuma Babu mai shiryar dashi. Kuma Ina Shaidawa babu abinda bautawa da Gaskiya sai Allah shi kadai, kuma ba shi da abokin tarayya. Kuma Ina Shaidawa Muhammad bawansa ne Kuma manzonsa ne._

_Bayan haka, insha Allah zanyi amfani da wannan daman da na samu yanzu nayi mana takaitaccen bayani akan *ZAKKAR FIDDA KAI*_

_Kamar yadda na sanar daku jiya cewa akwai wasu matsalolin da zai sa ku nemeni ku rasa a wannan zauren, tho amma sai nayi tunani cewa bai kamata ace na tafi banyi muku bayani akan wannan mas'alar ba, kasancewar yadda kuke aikomana da tambayoyi akansa, da kuma yadda muka sha bayani akan Watan Ramadan, tho bai kamata ace na tsalleke wannan bayani ba._

_Tho jama'a kusani Zakkar Fidda Kai Sadaka ce da Manzon Allah s.a.w ya farlanta ta yayin da aka gama azumi._

_An kira ta zakkar fidda kai ne saboda tana wajaba ne idan an gama Azumin Ramadan gaba daya._

_Zakkar Fidda kai wajibi ce akan dukkan musulmi, wanda ya mallaki sa'i daya na abinci (kamar kwano daya kenan) wanda ya fi yawan abin da zai ciyar da iyalansa._

_Mai ba da zakkar zai fitar wa da kansa, matarsa, da duk wanda ciyar da shi take kansa, har ma dan jaririn da yake cikin ciki._

_Dalilin wajabcinta shi ne abin da aka rawaito daga dan Umar Allah ya yarda da shi ya ce, “Manzon Allah s.a.w ya wajabta zakkar fidda kai, sa'i daya na dabino, ko sa'i dayan da sha'ir, an wajabta ta akan bawa, da Da, namiji da mace, babba da yaro daga cikin musulmi. Manzon Allah ya yi umarni a bayar da ita zakkar kafin mutane su fita sallar idi” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi]._

_An fi son a fitar da zakkar fidda kai ranar Idi, bayan alfijir ya bullo kafin sallar Idi. Kuma ya halatta a gabatar da ita kafin ranar idi da kwana daya ko biyu, saboda sahabbai sun yi haka._

_Ba ya halatta a jinkirta ta har bayan idi, saboda hadisin dan Umar wanda ya gabata in da yake cewa: Manzon Allah ya yi umarnin a ba da ita kafin fitar mutane zuwa sallar idi”._

_Haka ma a cikin hadisin Abdullahi dan Abbas, Manzon Allah s.a.w ya ce, “Wanda ya bayar da ita kafin sallar idi, to zakka ce karbabbiya, wanda kuwa ya bayar da ita bayan sallah, to sadaka ce daga cikin sadakoki” [Abu Dawud ne ya rawaito shi]._

_Kowane mutum sa'i (Sa'i dayan na Alkama yana daidai da kilo biyu da giram arba'in) daya ne, daga cikin abincin da dan mutane suke ci, kamar shinkafa, dabino, alkama, saboda hadisin Abu Sa'id Al-khuduriy Allah ya yarda da shi ya ce, “Mun kasance muna fitar da zakkar fidda kai daga abinci a zamanin Manzon Allah s.a.w ranar qaramar sallah”_

_Abu Sa'id ya ce, “Abincinmu a wannan lokaci kuwa shi ne Sha'ir da zabibi da cukwi [Cukwi: Shi ne nonon da ya bushe, a na girki da shi], da dabino" [Bukhari ne ya rawaito shi]._

_Ana bawa wadannan mutanen guda takwas zakkar fidda kai, saboda sun shiga cikin fadin Allah Madaukakin Sarki “Kadai Sadaka a bawa faqirai .......…”. (Attauba : 60) ba sai mun karasa ba duk kunsan mabukacin da ake bawa._

_Jama'a akwai hikimar Zakkar Fidda Kai, Amma bazai yiwu mu kawosu duka ba, amma zamu kawo guda biyu kawai daga cikin hikimar yinsa._

_1) Tsarkake mai azumi daga maganganun wofi da na batsa, saboda abin da aka rawaito daga Abdullahi dan Abbas Allah ya yarda da shi ya ce, “Zakkar fidda kai tsarki ce ga mai azumi daga maganganun banza da ayyukan batsa, kuma ciyarwa ce ga miskinai” [Abu Dawud ne ya rawaito shi]._

_Saboda mafi yawanci mai azumi ba ya rabuwa da maganganun da basu da amfani da wasannin shirme, da maganar da ba ta da fa'ida, tho wannan sadakar sai ta zamar masa tsarki daga irin wadanncan maganganun haramun da ya yi, wadanda suke rage ladan ayyuka, suna rage azumi._

_2) Yalwatawa miskinai da talakawa, da wadatar da su ranar idi daga roqon mutane, roqon da yake dauke da kaskanci da wulakanci a ranar idi, wadda take rana ce ta farin ciki da murna, sai su yi tarayya da mutane cikin farin cikin ranar idi. Ina fatar angane da kyau?? Allah ta'ala yayi mana jagora._
=
=
_Dan uwanku a musulunci_ 
°
*_✍Abdulrasheed Ibn Musa Abms_*
°
°
.
Allah ta'ala yasa mudace
.
.
https://www.facebook.com/Zauren-Majalis-Sunnah-420869088334488/?referrer=whatsapp
.
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.

Post a Comment (0)