*Yau naga abin tausayi a Unguwar Takuntawa (Kano)*ðŸ˜
Akwai wasu Yan mata su uku Mahaifiyarsu ta mutu, Mahaifinsu ya mutu Babban wansu ya mutu duka a tsakanin wata biyu (2). Kafin Mahaifinsu ya mutu sana'arsa wanki da guga, suma yaran nasa mata guda uku irin wannan sana'ar suke sai suyi wanki Mahaifin yayi guga. Bayan ya rasu sun cigaba da wanki amma ba guga. Abin tausayin shine suna wanke kaya set daya (Zani, Riga da Dankwali) akan Naira Goma N10
Babbar ta fara Sakandire amma saboda halin Talauci bata gama ba tana SS2 ta fita tun fiye da shekaru 5 baya. Mai binta kuma ta gama Sakandire shekaru kusan 3 baya kuma bataci gaba ba, sai karamar da take a SS3. Kuma dukansu sunyi Makarantar Mata ta Gandun Albasa.
Gidansu dan karami ne daki biyu ne, bayan da Babansu da Babarsu suka rasu sai Yayarsu ta dawo Gidan ita da Minjinta suka zauna a Daki daya ragowar daki dayan shine Matan su 3 suke kwan a ciki tare da Yayan Yayar tasu suma su uku. Sannan a dakinsu ko Gado babu sai dai su kwanta a kayan wankin da aka kawo. Akwai wani dan gidan wata yayarsu shima da yake zaune a Gidan a wani dakin Langa-Langa. Bandakin Gidan babu ko rufi a bude yake, kafin wannan lokacin katangar Gidan Gajeriya ce ko wanka akeyi ana ganin kan mutum sai aka samu wani makocinsu ya kara musu bulo daya yayi musu fulasta
A yanzu gidan kofarsa ta karye sai dai a jingina ta idan dare yayi
Abin sha'awar shine duk mutanen unguwar suna fadin kyawawan halayensu. Ba kuma sa kula Samari kullum cikin shiga ta kamala ko fita basayi suna gida suna wanki.
Mai son ya taimaka musu zai iya tambayata Adireshin su ko ya tura ta wannan account
Hafizu Shehu Ringim
0688899543
Access Bank
*Taimako baya kadan, daure ka bada naka a wannan wata mai albarka*