MATSAYIN ZAKKA A SHARI'ANCE 20


_*⚖️MATSAYIN ZAKKA A' SHARI'ANCE⚖️*_(20)

*DUKIYOYIN DA BA A FITARWA ZAKKA:*

 Muna ganin ya kamata bayan mun zayyana dukiyoyin da ake fitar wa Zakka mu zayyana wadanda ba a fitar musu kamar haka:

 Na daya bayi,
da dawaki,
da jakuna,
da alfadarai. 
Saboda hadisin da Bukhari ya rawaito, wanda ya nuna haka.

 Na biyu dukiyar da ba ta kai nisabi ba.

 Na uku kayan marmari,
kamar su lemo, goba, ayaba da sauran su.

 Na hudu danyun kaya,
kamar su tattasai, tumatur,
kabewa da sauran su.

Sai idan a matsayin su na kayar sayarwa ne wadanda Kimar su ta kai nisabi kuma ta shekara.

Na biyar kayan ado na mata.
Watau gwal din sawa na mata, wanda ba a saya da niyar idan ya yi tsada a sayar ba.

 Na shida duwatsu masu alfarma,
kamar yaKutu da zamaraddu,
da lu’u-lu’u da sauran su. Sai dai idan ciniki ake yi da su. 

Na bakwai kadarori na ado kamar gidaje da kujeru da shimfidu da sauran su. 

(Duba FiKhu – Zakat juz’I na 2, sh: 547 – 548.)

_*Zamuci gaba insha Allah!!*_
Rubutawa>>✍🏼
*Abubakar Salihu Kabara*

Gabatarwa_
_*ALHUSEIN ABBAN SUMAYYA*_

*_Ga masu sha'awar bin shirye shiryrnmu ta Telegram se yabi ta_*👇🏽
https://t.me/miftahul_ilmi

Dan kasancewa damu ta
WhatsApp
_*Miftahul ilmi*_
Se a turo cikakken suna da Address ta wan nan Number👇🏽
07036073248
Post a Comment (0)