DALILIN YIN AURE

*SIRRIN MALLAKAN MIJINKzi*

*_Dalilin Yin Aure_*

Akwai dalilai da yawa da suka sa dole duk wani mutum mai hankali yayi aure idan yakai munzalin yin auren.

Annabin tsira (S.A.W) yace da al’ummarsa kuyi aure ku hayayyafa dan inyi alfahari da yawanku ranar qiyama. Sannan Allah SWT ya halicci mutane (maza da mata) da sha’awa, wacce hanya daya da duk addinai suka yarda da ayi amfani da ita wajen biyan buqatar sha’awa shine aure. Wadannan dalilai guda biyu ma kawai sun isa hujja ga masu cewa su basa soyayya; sai da soyayya ne za’a iya yin aure.

Idan aka duba bangaren ibada kuma, Annabi (S.A.W) yace wanda yai aure ya bayar da rabin ibadarsa, sannan duk wani abu da masu aure zasu yiwa junansu na daga jin dadi lada zasu samu, hmn wannan itace garabasa, hanya mai sauqi ta samun aljanna.

Yana da amfani mutum yasan wadannan manufofi na yin aure kafin yayi aure, sannan kuma ya dinga tuna su koda yaushe, musamman a lokacin da aka samu sabani, hakan zai taimaka wajen shawo kan da yawa daga cikin matsalolin aure.

Haka shima wanda yaje yin sulhu ga ma’auratan da suka sami sabani, yana da kyau ya tunantar dasu akan wadannan manufofi na yin aure; Allah yasa mu dace.

 
Wabillahi Taufiq.

Rubutawa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*

Gabatarwa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*


*- Zauren Macen Kwarai-*

*. Ga masu buqatar shiga Zauren Macen Kwarai sai a turo da cikakkiyar sallam tare da cikakken suna da Address ta wannan Number +2348036692586,08062828025 a WhatsApp.*

Post a Comment (0)