ILLOLIN BASIR


*SIRRIN MALLAKAN MIJINKI*

*_ILLOLI DA BASIR KAN HAIFARWA DAN ADAM_*
Basir ko kuma ince Dan kanoma wanda a Turance ake kira da "DYSENTERY" yana haddasa illoli da dama kamar haka :
*1.TSUWAR HANJI*
Zaka rinka jin hanjin cikinka na yawan tsuwa akowane lokaci.
*2.KUMBURIN CIKI* Cikinka zai kumbure saboda toshewar hanji a sanadin dattin ciki da yawaitar girman kwayoyin cuta da rashin samun damar abinci ya yi saurin narkewa.
*3.YAWAN TUSA* Zaka rinka yawan fitarda iska akai akai, wani iskan sai ka ce wanda ya ci mushe.
*4.ZAFIN JIKI DA CIWON KAI* Jikinka zai rinka zafi ga kuma yawaitar ciwon kai wanda baya jin magani kamarsu analgesic.
*5.RASHIN CIN ABINCI KA KOSHI* Basir na haddasa maka kaji baka iya cin komai,kusan komai kaci sai kaji ba dadi.Take ka koshi.
*6.YAWAN ZUWA TOILET* Basir kansa kayi ta yawon zuwa toilet,idan kaje kuma kayi ta faman yunkuri da nishi sai zafin musiba da fitar majina ko jini dan tsirit.
*7.RAMEWA* Basir kansa ka rame kamar mai ciwon qanjamau.
*8.CIWON GABOBIN JIKI* Basir kan haddasa ciwon jiki da kowace ga6a ta jiki.
*9.TASHIN ZUCIYA* Sai kaji kamar kayi amai,kana ta : zubarda yawu.
*10.FITAR BAYA* Duburarka zata fito waje (basir mai tsiro).
*11.CIWO A CIKIN DUBURA* Sai kaji matsanancin ciwo ka kasa tsayawa ko zama.
*12. DAUKEWAR SHAWA* Namiji yakasance kamar baima balaga ba, ita kuma mace batama san meye biyan bukata ba, duk tabi ta bushe ba ni'ima ba wata gamsarwa.
*13. KAIKAYIN DUBURA* Basir kansa dubura ta tsage ga zafi da fesowar kuraje.
*14.KURAJE GA MATSE MATSI* Basir kan haddasa irin haka amma mutane da dama suna tinanin kamar sanyi ne, to na sanyi ya sha banban dana basir, dan na sanyi akan ga zubar farin ruwa masu yauqi da wari kamar danyen kifi.
*15. YANA MURDE HANJI* Ta yanda zai haifarda ru6ewar hanji da sauran cutukan ciki.
*16. BAYAN GIDA MAI TAURI* Yana haddasa bayan gida mai tauri kamar duwatsu,kamar kashin dabbobi.

Wabillahi Taufiq.

Rubutawa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*

Gabatarwa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*


*- Zauren Macen Kwarai-*

*. Ga masu buqatar shiga Zauren Macen Kwarai sai a turo da cikakkiyar sallam tare da cikakken suna da Address ta wannan Number +2348036692586 a WhatsApp.*
Post a Comment (0)