TSUMIN KANKANA


*SIRRIN MALLAKAN MIJINKI*

*_Yadda Ake Hada Tsumin Kankana_*

Yar uwa duk abin da kika sani yana son gyara ya kamata ace kina ma kanki gyara don samar da ni'ima, koda ace kina da ni'ima yakamata ace ki dunga sha don tabbatar da ni'ima a jiki.

Zaki nemi abubuwan hadi kamar haka;
* Kankana
* Gwanda 
* Dabino
* Zuma 
* Ruwan kwakwa
*Bayani;* Zaki samu kankana ki yayanka sai gwanda sannan ki jika dabino bayan kin cire kwallon sai ki hadasu waje daya ki markadasu sai ki tace ruwan sannan ki zuba zuma da ruwan kwakwa ki gaurayashi ki ajiye zai iya kwana biyu bai baciba kuma zaki dunga sha safe da yamma.


Wabillahi Taufiq.

Rubutawa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*

Gabatarwa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*


*- Zauren Macen Kwarai-*

*. Ga masu buqatar shiga Zauren Macen Kwarai sai a turo da cikakkiyar sallam tare da cikakken suna da Address ta wannan Number +2348036692586 a WhatsApp.*
Post a Comment (0)