SABON SARKIN BOLLYWOOD
(MATASHIYA: Idan har kai ba masoyin Akshay Kumar bane to ka nemi rubututtukana guda biyu da suka gabata masu taken MAKOMAR JARUMI SHAH RUKH KHAN A BOLLYWOOD da kuma WAYE ZAI MAYE GURBIN SHAH RUKH KHAN A MATSAYIN SABON SARKIN BOLLYWOOD, hakan shi zai sa ka fahimci wannan rubutun)
Na san cewa mutane da dama za su yi mamakin jin yadda na faɗo sunayen manyan jarumai a rubutuna da ya gabata tare da bayyana dalilin rashin cancantarsu na maye gurbin jarumi Shah Rukh Khan a matsayin sarkin Bollywood bayan ya yi murabus. Sannan in mai karatu ya lura da kyau zai ga cewa na sakaya sunan wanda nake tunanin shi ne zai iya ɗarewa kan wannan karaga, to na yi hakan ne saboda wannan rubutun.
Wato ko da yake shi ɗin ba laɗifi bane, ba waliyyi bane kuma ba mutum ne da na yarda da nagartarsa ɗari-bisa-ɗari ba, maganar gaskiya ita ce jarumi Srk ya wuce yadda duk mutum yake tsammani in dai a harkar fim ne, ya riga ya shanye tunanin mutane don haka duk mai son yin gardama please su haɗu da keyboard ɗinsa su yi.
Don haka tambayar dai ita ce: WAYE ZAI MAYE GURBIN JARUMI SHAH RUKH KHAN A MATSAYIN SABON SARKIN BOLLYWOOD? A halin yanzu babu wanda zai iya hawa kan wannan karaga ya zauna daram kuma a zauna lafiya face mutum ɗaya jal! Kuma ba kowa bane face jarumi Akshay Kumar wato "The Khiladi Of Bollywood". Amma kafin ka yanke hukunci, karanta waɗannan jawabai masu zuwa:
Mun riga mun ga tashe da shahara irin ta "The Shahenshah of Bollywood wato Amitabh Bachchan, mun ga Soyayya, ƙwarewa da kuma shahara irin ta King Khan wato Shah Rukh Khan, sannan mun ga tashe da wadaƙa da kuɗaɗe a box office irin na Sultan wato salman Khan. Hallau mun ga ƙwarewa irin ta Perfectionist wato Aamir Khan, kamar yadda muka ga tashe da amincin nagartar aiki irin na duggu wato Hrithik Roshan, ga shi yanzu muna kallon gwaninta irin ta bigire na uku daga ahalin Kapoor wato Ranbir Kapoor tare kuma da bunƙasa irin ta Ranveer Singh.
Amma akwai wani mutum ɗaya wanda ya dage tun daga 90s har zuwa yanzu bai sassauta ba, kuma wanzuwar waɗancan jiggan jarumai bai hana shi fitowa ba, nasararsu ba ta hana shi samun nasara ba, sunansu da tashensu bai hana shi tasawa ba, sannan fina-finansu ba su hana nashi shiga zukatan 'yan kallo ba. Lallai Mr. Khiladi ya zama zakaran gwajin dafi a Bollywood. Sannan;
1.Shi ne jarumin da babu ruwan shi da sai a ranar hutu zai saki fim ɗin da zai iya kaiwa 100 crore. Babu ruwansa da ranar hutu ne ko ba ranar hutu bane, in dai lokacin yayi to kuwa zai saki fim. Hakan kuma bai hana fina-finansa samun kasuwa ba, balle kuma yanzu da ya gane wa sakin fim a ranar Republic Day. (shin ko hakan ya tuno maka da wani jarumi a farkon shigowarsa Bollywood)
2. Shi ne kuma jarumin da bai damu ba da sai wani babban jarumi ko ƙasurgumin kamfani ya goyi bayan shirinsa ba domin ya samu nasara. (Shin ko ka tuna da wani jarumi?)
3. Sannan shi ne jarumin da bai damu da yayi karo da wani babban jarumi ba a box office (mun ga abinda ya faru a tsakanin Rustum da Mohenjo Daro).
4. Haka kuma Jarumi Akshay Kumar bai da ƙyamar mutane ko yaya suke, kuma a shirye yake da ya yi aiki da kowa in damar hakan ta samu. (fatan wannan batu ya kaɗa maka wata ƙaraurawa).
5. Shi ne kuma jarumin da ba ya tsoron fitowa a matsayin mugu ko mummunar sifa a fim kamar yadda wasu manyan jaruman ke tsoro. (Har na tuna da Darr da kuma 2.0)
6. A halin yanzu shi ne jarumi mafi nagartar tarihi a kaf Bollywood, abu ne mawuyaci ka ji an ce ya shiga wata cakwakiya ko kuma ana Alan-baku da shi ko kuma ba sa shiri da wani. (fatan kun gane banbancin)
7. A tsawon shekaru kusan 25 da yayi a harkar kusan babu fannin da bai taɓa ba, action, romance, comedy, drama d.s Kenan kun ga ba za a yi masa gorin cewa abu ɗaya kawai ya iya ba.
8. Akshay Kumar ba ya shan taba kuma ba ya shan giya, sannan ba kamar sauran jarumai masu son ace suna da gurayen ciki ba, shi kullum zan-zan yake bawai gurayen cikin ne kawai suka dame shi ba.
9. Mutum ne shi da yake da sauƙin kai matuƙa kuma idan yayi kuskure yakan fito fili ya bayyana rashin dacewar hakan tare da bada haƙuri. (dogarinsa ya taɓa dukan wani ya fito ya bada haƙuri)
10. Akshay Kumar ya ɗauki aikinsa da muhimmancin gaske, hakan yasa ya ke iya yin fina-finai uku zuwa huɗu a shekara ba tare da tsoron ai za su rusa masa kasuwancin fina-finansa ba.
11. Shin ko kun san cewa ma duk da sakin fina-finai da yake yi da yawa a shekara wannan jarumin a yanzu shekararsa bakwai kenan babu wani fim nasa da ya faɗi a kasuwa? Ashe kuwa ba abin mamaki bane kuwa da ake ce masa "Garanti Kumar".
A taƙaice dai masu karatu, a halin yanzu babu wanda yake da ƙwazo, naci, juriya, haƙuri, nagarta, iya mu'amala da mutane, ƙwarewa da sanin ya kamata gami da cancantar hawa karagar sabon sarkin Bollywood face Jarumi Akshay Kumar!
Kamar yadda na faɗa a baya, idan garda kake jin yi, please ga ka keyboard ɗinka nan, amma in tattauna kake son a yi bismillah.
AKKIANS NA ALFAHARI DA KU!!!
©️✍🏻
Jamilu Abdurrahman
(Mr. Writer)
+2348185819176
Haimanraees@gmail.com