TAMBAYA TA 82


WANDA YAKE GIDA, ZAI IYA HADA SALLOLI SABODA RUWAN SAMA ? 

Tambaya:
Assalamu alaikum. Allah karawa malam ilimi da fahimta. Shin da Allah malam ko mutum zai iya hada sallah shi kadai idan ana ruwa bashi da ikon zuwa masallaci?. Nagode malam.

Amsa: 
To dan'uwa malamai sun yi sabani akan wannan mas'alar zuwa maganganu guda biyu :
I. Ya halatta ga wanda yake a gida ya hada salloli saboda ruwan sama, tun da ruhusa ce Allah ya bawa mutane, don haka ta shafi kowa da kowa, wannan ita ce maganar Hanabila kamar yadda Mardawy ya ambata a INSAAF 2\340.
2. Bai halatta ga wanda bai je sallar jam'i ba ya hada salloli saboda ruwan sama, saboda an yi sauki ne ga wadanda za su je masallaci don kar su jika jikinsu da ruwa, wannan wahalar kuma babu ita ga wanda ya yi sallah a gida, don haka rahusar ba za ta same shi ba, sannan kuma shari'a ta yi nufin ta kiyaye sallar jam'i shi ya sa ta saukaka wajan hada salloli a ruwan sama,don kar mutane su watse sallar jam'i ta tozarta, wannan ita ce maganar Imamu shafi'i a littafinsa Al'umm 1\195
A fahimtata maganar karshe ta fi inganci, don haka wanda yake gida ba zai hada salloli ba.
Allah ne mafi sani 

*Dr. Jamilu Zarewa.*
9/11\2015

*Irshadul Ummah WhatsApp.*
*08166650256.*
Post a Comment (0)