YADDA AKE HAƊIN PLANTAIN


*SIRRIN MALLAKAN MIJINKI*

*_Yadda Ake Hadin Plantain Mai Ciko Da Nono_*

Yar uwa nono yana daga cikin abun da Allah yayi ma mace baiwa wanda yake jan hankalin dan namiji.

Yar uwa in kika bari nononki ya kwanta to kina cutar da kanki ne domin zai rage miki kima da daraja a wajen mai gida, don hada wannan hadin zaki nemi kayan hadi kamar haka;
* Garin plantain (ayaba)
* Aya
* Gyada 
* Peak milk
*Bayani;* Zaki samu ayaba (plantain) ki yanyankata ta bushe sannan ki daka yayi garin to sai ki samu aya ki wanketa ki saka gyada ki sa amarkada miki sai ki tace ruwan kina diban wannan garin plantain din kina zuba madara peak kinasha kamar sau biyu arana kafin sati daya zakiga canji sosai nononki zasu tashi su ciko.


Wabillahi Taufiq.

Rubutawa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*

Gabatarwa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*


*- Zauren Macen Kwarai-*

*. Ga masu buqatar shiga Zauren Macen Kwarai sai a turo da cikakkiyar sallam tare da cikakken suna da Address ta wannan Number +2348036692586 a WhatsApp.*
Post a Comment (0)