FASSARAR WAƘAR KHUDA HAAFIZ


FASSARAR WAƘAR KHUDA HAAFIZ (Title Track)


• Waƙa - Khuda Haafiz (Title Track)

• Shiri - Khuda Haafiz

• Harshe - Hindi - Hausa 

• Shekarar Fita - 2020

• Sauti - Mithoon

• Rubutawa - Sayeed Quadri

• Kamfani - Zee Music Company

Rerawa - Vishal Dadlani

• Fassarawa - Jamilu Abdurrahman 


• Hum Milenge Phir Kisi Din

Za mu sake haɗuwa watarana. 

• Tab Talak, Khuda Haafiz

Kafin wannan lokaci, Allah ya kare ki. 

• Hum Milenge Phir Kisi Din

Za mu sake haɗuwa watarana. 

• Tab Talak, Khuda Haafiz

Kafin wannan lokaci, Allah ya kare ki. 

• Yeh Judaiyaan Hai Kuch Din

Rabuwa za ta zamo na 'yan kwanaki ne (kawai) 

• Tab Talak, Khuda Haafiz

Kafin wannan lokaci, Allah ya kare ki 

• Pal Yeh Beet Jayega

Waɗannan lokutan za su shuɗe. 

• Pyaar Laut Aayega

Ƙauna kuma za ta dawo. 

• Waqt Ka Behta Yeh Dariya Fir Kinaare Layega

Wannan kogin lokutan zai kai mu zuwa gaɓa da sannu. 

• Yaad Rakhna Mujhko Mohsin

Kada ka manta da ni ya Mai kyautatawa. 

• Tab Talak, Khuda Haafiz

Kafin wannan lokaci, Allah ya kare ki 

• Yeh Judaiyaan Hai Kuch Din

Rabuwa za ta zamo na 'yan kwanaki ne (kawai) 

• Tab Talak, Khuda Haafiz

Kafin wannan lokaci, Allah ya kare ki 

• Khuda Haafiz... Khuda Haafiz…

Allah ya kare ki... Allah ya kare ki. 

• Tu Meri Yaadon Ke Ghar Mein

A cikin gidan tunanuka na. 

• Har Ghadi Maujood Hai

Ki ka kasance a koyaushe. 

• Tu Meri Yaadon Ke Ghar Mein

A cikin gidan tunanuka na. 

• Har Ghadi Maujood Hai

Ki ka kasance a koyaushe. 

• Mere Zehen Mein Tujhse Juda

A ruhina da ke haɗe da ke. 

• Har Pal Kahin Mehfoos Hai

Kowace daƙiƙa tunaninki ajiye yake a ruhina. 

• Pal Yeh Beet Jayega

Wannan lokacinma kansa zai shuɗe. 

• Dil Se Tu Na Jayega

Amma ba za ki taɓa barin zuciyata ba. 

• Waqt Bhi Karle Yeh Koshish Waqt Haar Jaayega

Lokaci ma kansa idan ya yi yunƙurin goge ki daga tunanina, ba zai iya ba. 

• Hum Milenge Phir Kisi Din

Za mu sake haɗuwa watarana. 

• Tab Talak, Khuda Haafiz

Kafin wannan lokaci, Allah ya kare ki 

• Yeh Judaiyaan Hai Kuch Din

Rabuwa za ta zamo na 'yan kwanaki ne (kawai) 

• Tab Talak, Khuda Haafiz

Kafin wannan lokaci, Allah ya kare ki 

• Khuda Haafiz... Khuda Haafiz…

Allah ya kare ki... Allah ya kare ki. 


ƘARIN HASKE: Khuda Haafiz ko Khuda Hafiz tana ɗaukar ma'anoni a ƙalla guda biyu, "Allah ya tsare ka/ki" da kuma " Sai anjima". To a wannan fassara na zaɓi ma'anar farko ne kaɗai bisa ganin dacewarta da wannan waƙa ba don in kore ɗayar ma'anar ba 

©️✍🏻
 Jamilu Abdurrahman 
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com

Post a Comment (0)