HUKUNCIN MATAR DA KE QAURACE WA MIJINTA A SHIMFIDA



HUKUNCIN MATAR DA KE QAURACE WA MIJINTA A SHIMFIDA

https://chat.whatsapp.com/IZhc4HXjGXFDOuOmx3ceZA

*TAMBAYA*❓

Assalamu alaikum malam barka d dare malam miji nane na nemi y biya min bukata se yace bazayayi ba toh senace mishi nasan zezo yace nima yanason in biya Masa tasa bukatar toh bazanyi ba shine yace toh kada Allah yasa inyi din toh malam idan yazo na hanashi nayi laifi Koh inada zunubi?

*AMSA*👇

Wa'alaikumus salam, Æ´ar uwa a gaskiya abin da Shari'a ta nuna shi ne bai halasta mace ta qaurace wa mijinta a shimfiÉ—a ba ko da ya É“ata mata rai matuqar ya kiyaye haqqoqinta da Allah ya wajabta masa, saboda hadisi ya tabbata daga Abu Hurairah Allah ya qara masa yarda ya ce: Manzon Allah ï·º ya ce:
"Idan namiji ya kira matarsa zuwa shimfiÉ—arsa sai ta qi, har ya kwana yana fushi da ita, to Mala'iku za su yi ta tsine mata har wayewar gari".
Bukhariy 3237, Muslim 1436.
Saboda haka lallai mata su guji qaurace wa mazajensu a lokacin da suka buqace su, saboda kauce ma wannan tsinuwa na Mala'iku, su kuma mazaje su ji tsoron Allah su daina quntata wa matayensu.
Abubuwan da suke zama uzuri ga macen da mijinta ya neme ta ta qi su ne, kamar mace tana jinin haila, ko jinin biqi, ko rashin lafiyar da idan ta yi jima'i za ta cutu, ko abin da ya yi kama da haka na uzuri karɓaɓɓe a Shari'a, sai dai shi jinin haila da na biqi ɗin suna hana saduwa ne, amma ba sa hana jin daɗi daga abin da ke saman gyauto.
Allah S.W.T ne mafi sani.

Zaku iya samu wannan group na Facebook ta wannan hanyar👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Join us on Facebook🖕
Post a Comment (0)