LOKUTAN SALLAH


*أوقات الصلاة ١*
=
=
*LOKUTAN SALLAH 01*
.
.
*DAGA ZAUREN*
.
*MAJALIS - SUNNAH*
.
.
*ﻣﺠﻠﺲ ﺍﻟﺴﻨﺔ*
📓📔
Watsaps
⌨09032091131
+237665087032
.
.
.
Yau 02/ 09/ 1442
15/ 04/ 2021
=
Fitowa ta farko
=
=
*ﺇِﻥَّ ﺍﻟْﺤَﻤْﺪَ ﻟِﻠَّﻪِ، ﻧَﺤْﻤَﺪُﻩُ ﻭَﻧَﺴْﺘَﻌِﻴﻨُﻪُ، ﻣَﻦْ ﻳَﻬْﺪِﻩِ ﺍﻟﻠﻪُ ﻓَﻠَﺎ ﻣُﻀِﻞَّ ﻟَﻪُ، ﻭَﻣَﻦْ ﻳُﻀْﻠِﻞْ ﻓَﻠَﺎ ﻫَﺎﺩِﻱَ ﻟَﻪُ، ﻭَﺃَﺷْﻬَﺪُ ﺃَﻥْ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻟَّﺎ ﺍﻟﻠﻪُ ﻭَﺣْﺪَﻩُ ﻟَﺎ ﺷَﺮِﻳﻚَ ﻟَﻪُ، ﻭَﺃَﻥَّ ﻣُﺤَﻤَّﺪًﺍ ﻋَﺒْﺪُﻩُ ﻭَﺭَﺳُﻮﻟُﻪُ*
_Godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin sarki, Tsira da aminci Allah su kara tabbata ga Annabi Muhammad s.a.w da alayensa da sahabbansa baki daya._

_Bayan haka, jama'a wannan wani babi ne mai girman gaske duk da cewa dukkan wadannan bayanai suna da matukar muhimmanci. Su lokutan sallah saninsu yana da matukar muhimmanci, domin ba'a yin sallah sai lokacinta yayi kuma ba'a bari lokacinta ya fita ba'a yi ba, asali ma shigar lokaci sharadi ne daga cikin sharuddan sallah kamar yadda bayanai suka gabata kuma mukace da izinin Allah zamu kawo bayanai akan abinda ya shafi lokutan sallah._

_Lokutan Sallah:- Kowacce sallah daga cikin wadannan salloli wajibabbu guda biyar tana da lokacinta da Allah madaukakin sarki ya iyakance mata ba za'a yi ta kafin lokacinta yayi idan kuma lokacin yayi ba za'a bari sai ya fita ba, Allah madaukakin sarki yana cewa ''LALLE ITA SALLA TA KASANCE AKAN MUMINAI WAJIBICE KUMA ABAR GAYYADEWA LOKACI'' Suratun Nisa'i aya ta:103. Umar dan Khaddab Allah ya kara masa yarda yana cewa Sallah tana da lokaci da Allah ya sanya bata inganta sai a wannan lokacin'. Sallah tana zama wajibine idan lokacin ya ya shiga kamar yadda ayoyi masu tarin yawa suka nuna, gaba dayan malamai sun yi ijima'I akan falalar dake cikin yin sallah a farkon lokaci a dunkule, Allah madaukakin sarki yana cewa:- "KU YI RIGE-RIGEN AIKATA ALHERI". Bakara aya ta 148, wanda yake sallah itace babba akan dukkan wani alheri da musulmi zai gabatar. Kowacce sallah daga cikin salloli biyar din nan tana da lokacinta da Allah ya kayyade mata wanda kuma yayi daidai da halin da bayinsa suke, ta yadda zasu gabatar da wadannan salloli akan lokutansu ba tare da wani abu ya tsare su ba asalima zata taimaka musu ne, kuma ta kankare musu zunubai, ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya kamantata da ruwa da yake gudu wanda mutum a kullun yake wanka a cikinsa sau biyar kana tsammanin zaka ga wani datti a tare da shi!._

_1. Lokacin Sallar Azahar: Lokacin sallar azahar shine daga lokacin da rana ta karkata daga tsakiyar sama ta koma zuwa bangaren yamma, zaka gane hakane ta yadda inuwarka zata koma bangaren gabas bayan ada baka ganta ba. Wato yadda al'amarin yake alokacin da rana take gabas zaka ga inuwa ta na yammane, lokacin da rana take kara dagowa lokacin inuwar take kara ragewa har zuwa lokacin da rana zata zo tsakiyar sama daidai, za kuma ta dan tsaya kadan, tho a daidai wannan lokacin da take a tsakiya cif zaka ga ba wata inuwa, domin sai ranar ta karkata wani bangarene sannan inuwar ta bayyana a wani bangaren. Tho daga lokcin da ranar ta cigaba da tafiya zuwa yamma tho daga lokacin inuwa zata cigaba da bayyana bangaren gabas, ranar tana kara yin yamma inuwar tana kara tsawo bangaren gabas. Daga lokacin da ranar ta karkata zuwa bangaren yamma kuma alamar hakan itace ka ga inuwarka ta bayyana bangaren gabas tho da ganin haka lokacin sallar azahar yayi, ba abinda ya rage sai dai a sallah ce ta, sai dai idan lokacin ana fama zafin rana sai a jinkirta kadan, ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yana cewa: ''Idan zafi ya tsananta tho ku dan sanyaya sallah, domin tsananin zafin nan daga nunfashin jahannama ne''. Bukhari da Muslim da Malik a Muwatta'u. Wannan shine loakcin sallar azahar har kuma zuwa inuwar komai ta zama kamar tsawonsa._

_Kunga kenan anan ba wata sallah mai suna karfe biyu ko karfe daya, kamar yadda lokuta suke canzawa a tsawon shekara tho haka lokutan sallah suke canjawa, duk mun san wani lokaci magariba akan yita kusa bakwai na yamma wani lokacin kuma kusan shida da wani abu na yamma, tho ashe kamar yadda muka yarda lokacin magariba yana canzawa tho hakanan na sauran sallolin, kuma fa duk wannan a wasu yankunane kadan fa domin inda mutum ya je hajji ko umarah a inda aka saukar da sallar tho da ya ga wani lokacin ma tuni karfe daya an gama sallah kuma da shi akayi ta, amma idan ya dawo gida yace sai ta nuna. Allah Ubangiji yasa mudace._

_Zamu dakata anan, a lekca ta gaba zamu dora daga lokaci na gaba._
.
=
=
Zamu dakata anan sai bayani na gaba Inshaa Allahu.
=
=
_Dan uwanku a musulunci da Sunnah_
°
*_✍🏻 Abdulrasheed Ibn Musa Abms_*
*_(ABU-MANAL)_*
°
°
https://www.facebook.com/Zauren-Majalis-Sunnah-420869088334488/?referrer=whatsapp
°
°
Allah ta'ala yasa mudace
.
.
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.
Post a Comment (0)