WADANDA YA HALASTA SU SHA AZUMI DA KUMA HUKUNCE HUKUNCEN SU



*MAKARANTAR AZUMI 012* //

 ```📌 WADANDA YA HALASTA SU SHA AZUMI DA KUMA HUKUNCE HUKUNCEN SU``` 

Yana daga cikin Rahamar Allah ga Bayin shi, da kuma sauki na Shari’a, da saukakawa da Addini yake dashi, sai Allah ya togace wasu É“angare na Musulmi da yin Azumi, ya kuma sanya musu wasu hukunce-hukuncen na musamman da suka dace da halayen su, to anan zamu ambaci waÉ—anda ya halasta su ajiye Azumi, da kuma abunda yake da alaka da hukunce-hukuncen su na Shari’a;

*1.   MARA LAFIYA* : Allah Ya halasta ga mara lafiya da ya sha Azumi a matsayin Rahamar Allah da saukakawar Sa gareshi.

*2 .   MAI HAILA DA MAI JEGO* : Malamai sun haÉ—u akan cewa bai halasta ga mai Haila da mai Jego suyi Azumi (kafin Jini ya dauke musu ba) sai dai su sha su rama daga baya, idan kuwa suka yi Azumi to azumin su bai yi ba.

 *3.   MAI CIKI DA MAI SHAYARWA* : anyi sassauci gare su, su ajiye Azumi amma sai idan suna jin tsoron kada jinjirin dake cikin su ya cutu ko kuma ÆŠan da take shayarwa, sai su ciyar da Miskini a kowace a rana a madadin wannan Azumin da suka sha, wannan shine yafi rinjaye kuma yafi zama daidai – In Sha Allah –  kuma itace fatawar Sahabi Abdullahi dan Abbas da Abdullahi dan Umar. 

 *4* .   *WANDA BAYA IYA AZUMI A KODA YAUSHE* : kamar wanda Shekaru suka riske shi, kuma ya zama baya iya yin Azumi – Namiji ne ko Mace – da kuma kamar mara lafiya wanda ciwon sa ya ki warkewa, kuma ya zama kowanne daga cikin su bazai iya ramawa ba idan akace sai ya rama saboda wannan gazawar tana nan a koda yaushe ne, to su abunda yake akansu shine su ajiye Azumi sai su ciyar da Miskini a kowace Rana, dalili akan haka abun da aka ruwaito daga Abdullahi dan Abbas – Allah ya kara musu yarda – yace: (Tsoho da tsohuwa waÉ—anda ba zasu iya yin Azumi ba, ya halasta su sha Azumi, su ciyar da Miskinai a maimakon kowani wuni). [Bukhaariy ne ya ruwaito shi], ana iya duba littafin Sharhussunah ta Imamul Baghawiy 6/316 domin ganin gamsassun bayanai kan wannan mas’alar, hakan shine daidai In sha Allahu.

✍ *ANNASIHA TV*
Post a Comment (0)