DA GASKENE MAZAJEN ALJANU SUNA AUREN MATA DAGA CIKIN MUTANE?
https://chat.whatsapp.com/KeXayNmsBie671pMAKT9xN
*TAMBAYA*❓
Assalamu alaikum sir Dan Allah yarinya CE budurwa aljanu suka shigeta anje wajen wani malami da yazu kanta yafara rukiya sai aljani yace ya aureta waihar sunhaifu da ita yaran su hudu(4)fa. Wai sir a nasamun haka ne ? Inhaka ne to amtsayi bazawar take kenan ?
Kuma bawanda yasan ta tabayi ciki fa sir
*AMSA*👇
Wa alaikumus salam warahmatullahi wabarakatuh Sir. Alhamdu lillahi rabbil aalamin.
Wassalatu wassalamu ala rasulillah.
Da farko dai wace alama ta tabbatar maku da cewa aljani ya shigeta?
Na biyu wane irin Mallamin ruqya kuka samu?
Aljanin da bakin shi yace suna da haihuwa hudu da ita? Ko Mallamin ne ya fadi maku haka?
Toh ko ma wannene ya faru, ba wata aya ko wani ingantaccen hadisin da ya tabbatar da faruwar haka. Ma'ana haka haka baya faruwa, dangantaka ta jini tsakanin jinsin mutum da jinsin aljan.
Allah ya umarce mu da muyi hukunci da abin da ya baiyana gare mu.
(إِنَّاۤ أَنزَلۡنَاۤ إِلَیۡكَ ٱلۡكِتَـٰبَ بِٱلۡحَقِّ لِتَحۡكُمَ بَیۡنَ ٱلنَّاسِ بِمَاۤ أَرَىٰكَ ٱللَّهُۚ وَلَا تَكُن لِّلۡخَاۤىِٕنِینَ خَصِیمࣰا)
[Surat An-Nisa' 105]
Saboda haka yarinya tana nan a matsayin ta na budurwa, ba bazawara ba. Idan ka kira ta bazawara, ka zalunce ta. Allah ya hana mu magana da ka
(وَلَا تَقۡفُ مَا لَیۡسَ لَكَ بِهِۦ عِلۡمٌۚ إِنَّ ٱلسَّمۡعَ وَٱلۡبَصَرَ وَٱلۡفُؤَادَ كُلُّ أُو۟لَـٰۤىِٕكَ كَانَ عَنۡهُ مَسۡـُٔولࣰا)
[Surat Al-Isra' 36]
Maganar ka ta karshe cewa ba wanda ya san ta taba ciki, ban gane abin da kake nufi ba. Amma idan kana nufi cikin aljani, toh sai ku jira kuga abin da zata haifa, idan jinjirin bil adama ne, ba Dan aljani bane, kuma ba aljani bane yayi mata cikin ba. Idan kuma jinjirin aljani ne, toh sai ku jira yazo ya dauki Dan shi don ya hada shi da sauran Yan uwan shi.
Wallahu ta'ala a'lam
Amsawa.
Mal Aliyu Masanawa.
Ga ma su sha'awar shiga wannan group sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu ta WhatsApp
08087788208
08054836621
*_Group Admin: 👇_*
*MAL. HAMISU IBN YUSUF*