KA KEWAYE KANKA DA ABOKANAI NAGARI



KA KEWAYE KANKA DA ABOKANAI NAGARI.
-
"Abokanai nagari sune irin abokanan da zaka kewaye kanka dasu a wannan duniyar, domin lallai suma suna da tasiri a lahirarka, musamman idan suna taimaka maka ko kuna taimakawa juna wajen ƙarfafar juna da yiwa juna wasici da jin tsoron Allah maɗaukakin sarki"
-
"Ka kiyayi yin abokantaka da mutanen banza, domin babu abinda zasu haifar maka saidai rikici da lahirarka, kai dasu duk babu wanda zai amfani kowa ta fuskar yiwa juna wasici da jin tsoron Allah, da kuma aikata kyawawan aiyuka nagari, to haƙiƙa wannan abokantakar babu abinda yake biyo bayanta face nadama a ranar lahira"
-
"A maimakon ka kasance da aboki wanda bazai kusantar dakai ga Allah ba, yafi dacewa ka kasance kai kaɗai ba tareda wani aboki ba, domin lallai haƙiƙa tabbas kasancewa tareda mutanen kirki kullum yakan daɗa kusantar dakai izuwa ga Allah, amma tarayya da mutanen banza kuwa kullum takan daɗa nesanta ka ga Allah ne, to kayi ƙoƙari koda yaushe ka kasance tareda abokanai na ƙwarai, domin kuwa abokantakar da akayi ta ba domin Allah ba a wannan duniyar takan zama abokanaiyyar gaba a ranar ƙiyamah"
-
Biyo Instagram É—inmu
https://instagram.com/hausa.islamic.pictures.quotes?igshid=11g6c9k6osqg5
-
Telegram channel
https://t.me/hausaislamicpicturesquotes
Post a Comment (0)