MENENE BAN BANCIN ANNABI DA MANZO

*_السلام عليكم ورحمة الله وبركا ته_*
➖➖➖➖➖➖➖➖
*_” بسم الله الرحمن الرحيم_*

_*Daga zauren*_
_*📚Ana- muslim📚*_
.



.
_*TAMBAYA:*_
:
MENENE BAN BANCIN ANNABI DA MANZO
:
_*AMSA:*_
:
_Malamai sunyi maganganu dayawa akan banbancin Annabi da manzo._
_Dukkan manzo Annabi ne amma ba dukkan Annabine manzoba._

_Banbancin Annabi da manzo shine:_
Manzo shine wanda Akaiwa wahayin Shari'a sabuwa aka umarce da isar da ita, 
Annabi shine wanda akaiwa wahayin shari'a amma ba'a Umarceshi ya isar da ita ga mutane ba, saidai wannan ban-bancin baya kubuta daka matsala da rikitarwa,
     Domin Annabi ma An Umarceshi da Da'awa dakuma Isarda sako ga mutane, dakuma hukunci,         
      _saboda haka Shaikul Isalam Ibnu taimiyyah yace:_
Abunda yake dai-dai Shine: Manzo shine: wanda aka aiko zuwa wasu mutane kafirai Wadanda suke karyatashi.

Annabi Kuma shine: Wanda aka aiko zuwa wasu mutane muminai da shari'ar Annabinda yagabaceshi yasanardasu yayi musu hukunci, kamar yanda Allah madaukakin Sarki yace:
*( إنا أنزلنا التورة فيها هدى ونور يحكم بها النبيون الذين أسلموا)*
Mun saukarda Attaura acikinta akwai shiriya da haske Annabawa Suna hukunci da ita, gawadanda Suka Mika wuya, sukai imani
Annabawan Banu Isra'ila Suna Hukunci da Attaurar da Aka saukarwa Annabi Musa Alaihissalamu, Amma fadin Allah madaukakin sarki
(وخاتم النبيين)
Cika makin Annabawa
Dangane da Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi wasallam, baice cika makin manzanni ba.??
Saboda cika Manzanci baya Nufin cike Annabta, Amma rufe Annabci yana Nufin cike Manzanci da Annabta saboda haka Annabi sallallahu Alaihi wasallam yace:
( Babu Wani Annabi Abayana) Baice ( Babu wani Manzo Abayana ba).
Saboda yasan Babu wani manzo ko Annabi abayansa shine cika makin Annabawa da Manzanni Sallallahu Alaihi wasallam.
Wallahu A'alamu.
:
```Allah ta'ala yasa mudace```
:
_*©​​✍🏽 ​​Sadeeq Ñagogo{βluñgu}​​​​*_
:
_*ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.​​*_
*--------------------------*
*_​•Ga mai sha'awar shiga Zauren 📚Ana -muslim_​*📚
_*​ta whatsApp sai yayi cikakkiyar sallama tare da suna da Address nasa zuwa⬇ ga lambar mu*_​​​​   
      _*08093347777*_
 _*08085777555*_   
〰〰〰〰〰〰〰〰〰 _*Doмιɴ ѕнιɢα ѕнαғιɴмυ ɴα ғαcєвooк ѕαι α lαtsα ɴαɴ*_ ⬇
https://www.facebook.com/Ana-Muslim-Group-156263338266984/
        ​
Post a Comment (0)