(POST TERM PREGNANCY)
Kamar yadda aka sani yawancin juna biyu daga samunsa zuwa haihuwa ba kasafai yafi wuce sati 37 xuwa 42 ba, amma wasu sukan wuce hakan wanda a turance akan ce (post-term ko past due) a hausance kuma ace shekarau. Amma Wannan takan faru a mataye kadan.
ABUBUWAN DA YA KAMATA AYI!!!
Tun daga lokacin da aka sami juna biyu ya kamata ace mace tana samun kyakkyawar kulawar likita musamman masu haihuwar fari.
ME KE JAWO HAKAN???
Mace ka iya fuskantar yanayin wucewar lokacin haihuwa bata haihu ba in ya kasance;-
1.An sami kuskure wajen lissafi inda wasu ke mance lissafin su riga debe karshe har su fara tunane-tunane akan sun wuce lokacin haihuwa wanda kuma ba hakan bane. Ana fara kirga cikine daga ranar da al'ada ta tsaya kamar yadda adadin kwanakin ya bambanta.
2.Idan mace ta zamto mai kiba/te6a (obesity).
3.idan ciki ya zamto shine na farko bata ta6a haihuwa ba (primigravida).
4.idan jaririn ya zamto namiji ne. Wato Maza ne Kän wuce lokacinsu yawanci.
5.Idan kin taba yi abaya za'a iya maimatawa.
6.idan ya zamto a dangi akwai wadanda suka fuskanci hakan akwai yi wuwar wani ma ya samu.
7.idan ya zamto mabiyiya ta sami matsala musamman dab da gabatowar wata na 9 lokacin haihuwa hakan Kän sa yaron ya rasa abunda ya ke samu musamman karancin iska (Placental problem).
8.shekaru idan ya zamto mace na dab da menopause wato dena haila gaba daya.
SHAWAR WARI
1.a daure afara xuwa awo daga zarar ciki yakai wata uku (4),
2.Yana kyau mu mazaje mu tabbatar muna basu kulawa tare da Samar musu da hutu yadda ya kamata.
3. Inda hali kake rakata zuwa awon da kanka hakan zaisa ta dada samun nutsuwa. °
4.Yawanci idan aka wuce sati 42 likitoci sukan yi binkice ai Ultrasound scan domin a tabbatar da lafiyar jaririn kalau, inda daga nan in aka ga lafiyar sa kalau akan kara ma mace lokaci zuwa sati biyu agani inda daga nan in bata haihu ba likita Kan yanke shawarar tsokano haihuwar wato (inducing).
1. Akan yi inducing din ta hanyar yin wata allura a cikin jijiyar jini.
2.Bada magani tai inserting agaban ta domin gurin ya zamto yai taushi.
3.Ko kuma ai aiki aciro inya zamto yaron yayi girma sosai ya yadda bazata iya haihuwa da kanta ba.
Lafiya Uwar Jiki