Yadda Ake Hadin Kwakwa Don Karin Ni'ima

*SIRRIN MALLAKAN MIJINKI*



*_Yadda Ake Hadin Kwakwa Don Karin Ni'ima_*
 

Zaki nemi kayan hadi kamar haka;
* Kwakwa
* Dabino
* Madarar peak
*Bayani;* Zaki samu kwakwanki ki fasa ki tsiyaye ruwan ciki, sai ki bare bawon ki gurza a magogi, ki markada bayan kin markada sai ki zuba ruwa, ki tace dusar daman a can gefe kin jika dabinonki sai ki markada shi, ki juye a cikin wannan tattaciyar kwakwar ki zuba madara peak sai ki dauko ruwan kwakwarki da kika fasa sai ki zuba madara ta gari cokali uku, sai ki juya ki saka a cikin firigi yayi sanyi ki dunga sha.

Wabillahi Taufiq.

Rubutawa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*

Gabatarwa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*

*- Zauren Macen Kwarai-*

*. Ga masu buqatar shiga Zauren Macen Kwarai sai su tura da cikeken sunansu tare daga in da take, ta wa'innan numba;* 👇 👇 👇

08162268959
Post a Comment (0)