ABUBUWA GUDA 33 DA SUKE TAIMAKAWA WAJAN SAMUN KHUSHU'I ACIKIN SALLAH
Darasi na Biyu-(2)
*11-Motsa dan yatsa manuniya alokacin Tahiya*
Manzon Allah ﷺ yana cewa:
*(Motsa yatsa manuniya acikin Tahiya,yafi tsanani ga Shaidhan fiye da bakin karfe)* kuma nuni dan tsaya manuni a cikin Tahiya,yana tunawa bawa Kadaitaka ta Allah da kuma ikhlasy da kyautata niyya ga dukkan ibada ga Allah shi kadai,kuma wannan shine mafi girman abinda shaidhan yake Qamata.
*12-Chanchanza nau'ikan surorin karatun sallah,da azkar da addu'i'in Sallah,yau idan kayi wannan gobe sai kayi wancan,kada ka zauna da yin nau'in zikiri ko addua ko sura guda daya kadai a kowace sallah.
*"Domin yin azkar da addua kala kala da chanchanza ayoyi da surori yana bata wata sabuwar ma'ana da hakan yake janzo nutsuwar zuciya da gabbai a cikin sallah,wanda wannan shine asalin KHUSHU'iN sallah"*
*13-Idan ya karanta ayar Sujada ta tilawa to yayi sujadar tilawa*
Allah yana cewa;
*(وَيَخِرُّونَ لِلْأَذْقَانِ يَبْكُونَ وَيَزِيدُهُمْ خُشُوعًا ۩)*
(Kuma sunã fãɗuwa ga haɓõɓinsu"suna sujada"sunã kũka,kuma yanã ƙara musu tsõro)
@الإسراء (109) Al-Israa
(أُولَٰئِكَ الَّذِينَ أَنْعَمَ اللَّهُ عَلَيْهِم مِّنَ النَّبِيِّينَ مِن ذُرِّيَّةِ آدَمَ وَمِمَّنْ حَمَلْنَا مَعَ نُوحٍ وَمِن ذُرِّيَّةِ إِبْرَاهِيمَ وَإِسْرَائِيلَ وَمِمَّنْ هَدَيْنَا وَاجْتَبَيْنَا ۚ إِذَا تُتْلَىٰ عَلَيْهِمْ آيَاتُ الرَّحْمَٰنِ خَرُّوا سُجَّدًا وَبُكِيًّا ۩)
(Waɗancan sũ ne waɗanda Allah Ya yi wa ni'ima daga Annabãwa daga zurriyar Ãdamu, kuma daga waɗanda muka ɗauka tãre da Nũhu,kuma daga zurriyar Ibrãhĩm da Isrã'ila,kuma daga waɗanda Muka shiryar kuma Muka zãɓe su.Idan anã karãtun ãyõyin Mai rahama a kansu,sai su fãɗi sunã mãsu sujada kuma mãsu kũka).
@مريم (58) Maryam
Manzon Allah ﷺ yana cewa:
*(idan dan Adam ya karanta ayar sujada kuma yayi sujada,sai Shaidhan yace:"Ya kaicona an umarci dan Adam da yayi Sujada sai yayi Sujadar,dan haka yana da aljanna,amma ni an umarceni da yin sujada sai bakiyi,dan haka wuta ta tabbata agareni")*
@ﺭﻭﺍﻩ ﻣﺴﻠﻢ.
*14-Neman tsarin Allah daga akan Shaidhan*
Shaidhan shine mafi girma makiyi agaremu wanda yake bayyana kiyayyarsa a fili kuma babu babban samun kariya daga wannan kiyayya tasa a gare mu kamar neman tsarin Allah akansa.
Babu lokacin da shaidhan yake bujurowa bawa kamar lokacin sallah dan ya bata masa sallah,ko ya rage masa daraja da ladarsallarsa har sai ya sanya masa wasi wasi da rabkannuwa dan sallarsa ta sami naqasa da rashin cikakkiyar lada,amma idan ka nemi tsarin Allah akansa to kayi maganinsa kuma zaka samu khushu'i mai girma acikin sallarka.
*Na neman tsarin Allah ne akan shaidhan acikin sallah a lokaci guda biyu*
Lokaci na farko
*lokacin adduar bude sallah,wannan adduar tana dauke da kariya da magance makircin shaidhan*
Lokaci na biyu
*lokacin da kaji kashiga wani tunani na duniya acikin sallah ko kashiga kokwanto,Sai kace AUZU BILLAHI MINASHSHAIDANIR RAJEM,sai kayu tofi guda ukku a bangaranka na hagu* insha Allah zaka sami waraka sai khushu'inka ya dawo kamar yadda kafara sallah.
Allah ne mafi sani
Mu hadu a Darasi na gaba insha Allah
https://chat.whatsapp.com/I8uQUDUSxpa3w9GwfMqHyv
SUBSCRIBE TELEGRAM CHANNEL:👇
https://t.me/DailyHadithss