Assalamu alaikum.
.
*Tambaya:*
Akwae wata yarinya tanada Yaya uwa¹ uba¹ abunda y faru shine: yarinyan tanada addini fiye d yayannata, shikuma yayan yanada sakaci akan sallah, hakan yana mawa ita kanwar daci a ranta.. Harta kae ga rashin jituwa tsakaninsu, daga karshe yayannata y mata gargadi d cewan karta kuskura ta sake shiga harkanshi, yakuma raba xumuncin dake tsakaninsu, hkn yasa ta fita dg sha'aninsa.. A takaece kenan Malam.
Tambayata anan shine:
Yaya hukuncin ibadarsu shi dkuma ita?
Shin itama tanada laefi?
.
*Amsa:*
A gaskiya kuskurene idan mutum yana aikata zunubi a guje shi ko a juya masa baya, domin yin hakan tamkar an bā wa shaiďan dama ne a kan shi. Abin da ya dace shi ne ta ci gaba da yi masa nasiha, ko ta sa wasu su yi masa waďanda ta san yana ganin girmansu. Sannan ta dinga roka masa shiriya a wajen Ubangiji.
Idan a dalilin hakan ya yi fushi yā yanke mu'amala da ita, to ai Aʟʟαн(ﷻ) yā ga zuciyarta, don haka ita ba ta da laifi, amma ta ci gaba da gaishe shi da girmama shi a matsayin yayanta, kuma ta rike shi a matsayin ďan uwa tare da ci gaba da yi masa addu'a da fatan shiriya.
Wallahu A'lamu.
.
*📚Irshadul Ummah WhatsApp.*
*+2348166650256.*
https://t.me/irshadulummah1
