MAZA SUNA DA HURUL-IN. MATA FA?



Wata mace ce take tambayar Malam Tana cewa:

Ku Maza kuna da "Hurul Iyn" mu kuma me gare mu?

AMSA: Babu banbanci tsakanin Maza da Mata wajen Aure a Aljanna, Aure yana daga cikin abeben da rai take so, Allah kuma yayi ma yan Aljanna al'kawarin wannan. 
وَفِيهَا مَا تَشْتَهِيهِ الْأَنفُسُ وَتَلَذُّ الْأَعْيُنُ ۖ وَأَنتُمْ فِيهَا خَالِدُونَ.

((Acikin Aljanna akwai ababen da rai take kwadayi, da ababen da idanuwa ke jin dadinsu...)). 
Don haka babu banbanci tsakanin Namiji da Mace wajen jin dadin rayuwar Aure a Aljanna. 

Ta sake cewa:
To amma fa AlQur'ani ya siffanta "Hurul Iyn" da siffofi na Musanman, amma kuma bai siffanta Mijin da Mace zata so ta Aure a Aljanna ba??

AMSA:
Maganarki gaskiyace, sai dai AlQur'ani yana magana da Mutane ne da gwargwadon abinda ransu take so kuma take kwadayi. Kinga Maza a Jumlace siffar Mace tana da muhimmanci a wurinsu, don haka sai aka wasafta musu ta Aljanna, Ita kuwa Mace abinda yafi muhimmanci a wurinta shine halaye da dabi'un Namiji da kyakkyawar mu'amalarsa gare ta.
Maza koda sun girma a Shekaru, to suna son Mace. Amma ita Mace idan girma yazo Mata, Lamarin Maza yana sauyawa a wurinta kwarai.
Don haka ma da Maza zasu zauna hira, to zancen Mata da Aure yana daga cikin abinda yake sanya su nishadi, wannan yasa AlQur'ani yayi musu magana da abinda ransu tafi so da kwadayi. A Lokacin da ita kuma Mace take da kunya da boye soyayyarta/kaunarta a wurin jama'a, don haka itama sai AlQur'ani ya girmama wannan dabi'a tata.

Da zamu lura da dillalan Kawalai na zahiri dana kafofin sada zumunta masu yada badala zamu ga Mace ita suke nunawa Maza don neman kudi, amma da wuya kaga ana tallata Namiji don Mata suzo su nemeshi!
To wannan shine tsarin rayuwa a haka akayi Mutane, cewa Namiji shine zai rika bin Mace ba Macece zata rika nemansa ba.
Don haka AlQur'ani ya dace da Fitrar Mutane.

Ta ce: Ai kuwa ban taba tunanin cewa AlQur'ani yana kula da dabi'u da halayen Mutane Mabanbanta ba.

AMSA: Tare da haka dole ki bada gaskiya cewa Allah madaukakin Sarki Adaline acikin hukuncinsa, baya zalunci, Annabi (SAW) yace:
...ما في الجنة أعزب

(Babu Gwauro ko Gwauruwa a Aljanna).

Tace: Haba dai, yau na fara jin wannan Hadisin.

AMSA:
 Kwantar da hankalinki, zaki Auri wanda kike so a Aljanna kuma za'a baki kyawun da yafi na "Hurul Iyn" sannan za'a baki Shekaru irin na Budurwa, saboda Aljanna gida ne da Allah ya tanada don ya sakankama bayinsa na kwarai, dadin cikinta baya yankewa.

•Mace tana da halaye Mabanbanta a Aljanna kamar haka:
i) Ko dai ta kasance ta Mutu gabanin tayi Aure a duniya, ko ta mutu bayan ta rabu da Mijinta, ko kuma ta samu Aljanna amma Mijinta yana Wuta (Wal Iyazu billah), to a nan Allah zai Aura mata Miji daga Mazan duniya wadanda suka shiga Aljanna.

ii) Ko kuma Mijin Mace ya mutu bata Auri wani ba bayansa, to a nan Allah zai daura mata Aure da shi Mijin nata na duniya.

iii) Ko kuma ya kasance bayan Mijinta ya mutu ta sake wani Auren, to anan Allah zai bata zabi acikin Mazajen, sai ta zabo wanda take so, ko kuma ya zabo wani na daban, ko kuma Allah ya zaba mata mafi kyawun dabi'unsu.

Abin nufi dai a kowane irin yanayin Mace ta Mutu, tana da Miji a Aljanna.

Ni'imomin Aljanna basu wasaftuwa, Annabi (SAW) yace, Allah Ta'ala yace:
أعددتُ لعبادي الصالحينَ ما لا عينٌ رأت ولا أذنٌ سمعت ولا خطرَ على قلبِ بشرٍ، اقرأوا إن شئتم فَلَا تَعْلَمُ نَفْسٌ مَا أُخْفِيَ لَهُمْ مِنْ قُرَّةِ أَعْيُنٍ جَزَاءً بِمَا كَانُوْا يَعْمَلُونَ.

((Na tanadawa bayina na kwarai, abinda Idanuwa basu taba gani ba, kunne bai taba ji ba, bai kuma taba darsuwa a zuciyar wani Mutum ba, ku karanta idan kun so: Rai bata san abinda aka boye mata na sanyin Idanuwa ba, sakamakone na abinda kuka kasance kuma aikatawa)). 

Shin Mace tana da gida a Aljanna?
Ina kyautata zaton wanda yace Mace ba zata Mallaki gida a Aljanna ba ya dogarane da cewa duk Mace tana da Miji, don haka gidan Mijinta shine gidanta.

AMSA: 
Tabbas duk Mace tana da Miji a Aljanna kamar yadda bayani ya gabata, to amma hakan baya nufin ba zata Mallaki gidanta na kashin kanta ba, saboda dalilai na Shari'a da suka zo da batun gidaje Mallakin Mata kamar Matar Fir'auna-Asiya- ta roki Ubangiji ya gina Mata gida a Aljanna kuma Allah ya karbi addu'arta. Ga Nana Khadija (RA) duk wadannan suna da gidajensu a Aljanna bayan na Mazajensu.

A karshe dai Aljanna gidane da ba'a yi ma bayi doka, kowa zai yi abinda yake so ba tare wani yaji haushin wani ba, ko ya tauye masa hakkinsa, kiyasin sa da gidan duniya kuskurene babba.

Allah yace:
وَنَزَعْنَا مَا فِي صُدُورِهِم مِّنْ غِلٍّ إِخْوَانًا عَلَىٰ سُرُرٍ مُّتَقَابِلِينَ.

Allah ya bamu Aljannar Firdausi don yalwatacciyar Rahamarsa.
Post a Comment (0)