HUKUNCIN GAISHE DA MARA LAFIYA DA FALALARSA 02



_*⚖ZAUREN MARKAZUS SUNNAH⚖*_

_*HUKUNCIN GAISHE DA MARA LAFIYA DA FALALARSA*_
                    

                _*DARASI NA BIYU*_

        _*FALALAR GAISHE DA MARA LAFIYA*_

_Da Sunan *Allah* Mai *Rahma* Mai *Jinqai*_

_*2. MALA'IKU SUNAYIN SALATI GA MAI GAIDA MARA LAFIYA:* Yana Daga Cikin Falalar Gaida Mara Lafiya Shine Mala'iku Zasu dingayiwa Wanda Ya Ziyarci Mara Lafiya Salati da Kuma Nema Masa Gafara daga Wurin Ubangiji. Hadisi Ya Tabbata *Manzon Allah (ﷺ)* Yana Cewa:_

ﻋَﻦْ ﻋَﻠِﻲٍّ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ ﻗَﺎﻝَ : ﺳَﻤِﻌْﺖ ﺭَﺳُﻮﻝَ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻳَﻘُﻮﻝُ: *”ﻣﺎ ﻣِﻦ ﻣﺴﻠِﻢٍ ﻳﻌﻮﺩُ ﻣُﺴﻠِﻤًﺎ ﻏﺪﻭﺓً ﺇﻟَّﺎ ﺻﻠَّﻰ ﻋﻠﻴﻪِ ﺳﺒﻌﻮﻥَ ﺃﻟﻒَ ﻣﻠَﻚٍ ﺣﺘَّﻰ ﻳُﻤﺴﻲَ، ﻭﺇﻥ ﻋﺎﺩَﻩُ ﻋﺸﻴَّﺔً ﺇﻟَّﺎ ﺻﻠَّﻰ ﻋﻠﻴﻪِ ﺳﺒﻌﻮﻥَ ﺃﻟﻒَ ﻣﻠَﻚٍ ﺣﺘَّﻰ ﻳُﺼﺒِﺢَ“*
```{رواه الترمذي}```

_An Kar6o Daga *Aliyu bn Abi-Dalib (ra)* Yace: Naji *Manzon Allah (ﷺ)* Yana Cewa: *“Babu wani Musulmi Wanda Zaiyi Sammakon Gaida Mara Lafiya, Face Mala'iku Dubu Saba'in (70,000) Suntayi Masa Salati Har Zuwa Yamma. Idan Ya Sake Ziyartar Mara Lafiya da Yamma Kuma Zasuyita Masa Salatin Har Zuwa Safiya...... ”*._
```{Tirmizi Ya Ruwaitoshi}```

_*3. RAHAMA DA GAFARA SUNA SAUKA GA MAI GAIDA MARA LAFIYA:* Gaida Mara Lafiya Tana Daga Cikin Hanyoyin da Ubangiji Ke Gafartawa Bawa Zunubansa tare Kuma Tausaya Masa. Hadisi Ingantacce Ya Tabbata Daga *Manzon Allah (ﷺ)* Yana Cewa:_

ﻋَﻦْ ﺟَﺎﺑِﺮٍ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ ﻗَﺎﻝَ: ﻗَﺎﻝَ ﺭَﺳُﻮﻝُ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ : ‏”ﻣَﻦْ *ﻋَﺎﺩَ ﻣَﺮِﻳﻀًﺎ ﻟَﻢْ ﻳَﺰَﻝْ ﻳَﺨُﻮﺽُ ﻓِﻲ ﺍﻟﺮَّﺣْﻤَﺔِ ﺣَﺘَّﻰ ﻳَﺠْﻠِﺲَ ﻓَﺈِﺫَﺍ ﺟَﻠَﺲَ ﺍﻏْﺘَﻤَﺲَ ﻓِﻴﻬَﺎ“*
```{رواه أحمد}``` ‏

_An Kar6o Daga *Jabir (ra)* Yace: *Manzon Allah (ﷺ)* Yace: *“Duk Wanda Ya Gaida Mara Lafiya, Bazai Gushe ba Yana Kutsawa Cikin Rahama ba Har Sai Ya Zauna. Idan Kuma Ya Zauna Zai Dulmiya Ne Acikinta”.*_
```{Ahmad Ne Ya Ruwaitoshi}```

_*4. SAMUN YALWA DA KUMA NI'IMTUWA DA ALJANAH:* Ubangiji Yayi Tanadin Gwaggwa6an Lada Ga Wanda Ya Kama Hanya Don Ziyartar Mara Lafiya. *Manzon Allah (ﷺ)* Yana Cewa a Cikin Ingantaccen Hadisinsa:_

ﻋَﻦْ ﺛَﻮْﺑَﺎﻥَ ﻋَﻦْ ﺍﻟﻨَّﺒِﻲِّ ﺻَﻠَّﻰ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻋَﻠَﻴْﻪِ ﻭَﺳَﻠَّﻢَ ﻗَﺎﻝَ : ‏”ﺇِﻥَّ *ﺍﻟْﻤُﺴْﻠِﻢَ ﺇِﺫَﺍ ﻋَﺎﺩَ ﺃَﺧَﺎﻩُ ﺍﻟْﻤُﺴْﻠِﻢَ ﻟَﻢْ ﻳَﺰَﻝْ ﻓِﻲ ﺧُﺮْﻓَﺔِ ﺍﻟْﺠَﻨَّﺔِ ﺣَﺘَّﻰ ﻳَﺮْﺟِﻊَ“*
 ```{ﻣﺴﻠﻢ: ٢٥٦٨}```

_An Kar6o Daga *Thaubãn (ra) Daga Annabi (ﷺ)* Yace: *“Lallai Idan Musulmi Ya Tafi Gaida Dan Uwansa (Mara Lafiya) Musulmi, Bazai Gushe a Gefen Aljannah ba Har Sai Ya dawo”.*_
```{Muslim: 2568}```

_*5. TUNAWA BAWA MUTUWA:* Ziyartar Mara Lafiya Yana daga Cikin Abubuwan dake Tunawa Bawa Shi Bakone a Wannan Duniyar Kada Ya Shagalta Ya Manta Akwai Tafiya a Gabansa. Hadisi Ya Tabbata *Manzon Allah (ﷺ)* Yana Cewa:_

ﻋﻦ ﺃﺑﻲ ﺳﻌﻴﺪ ﺍﻟﺨﺪﺭﻱ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ ﻗﺎﻝ : ﻗﺎﻝ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ : ‏*”ﻋﻮﺩﻭﺍ *ﺍﻟﻤﺮﺿﻰ، ﻭﺍﺗﺒﻌﻮﺍ ﺍﻟﺠﻨﺎﺋﺰ ﺗﺬﻛﺮﻛﻢ ﺍﻵﺧﺮﺓ “* 
```{ﺭﻭﺍﻩ ﺃﺣﻤﺪ}```

_An Kar6o Daga *Abi-Sa'idil Khudry (ra)* Yace: *Manzon Allah (ﷺ)* Yace: *“Ku Gaida Marasa Lafiya, Kuma Ku Dinga Halartar Jana'iza, Zasu Dinga Tuna Muku Lahira”.*_
```{Ahmad Ya Ruwaitoshi}```


_*YA ALLAH KA AZURTAMU DA LAFIYA KA KUMA BAMU IKON BAUTA MAKA DA LAFIYAR DA KA BAMU*_

_*✍🏼Abu-Aysha Al-Maliky*_

_ZAKU IYA BIBIYAR MU TA WAƊANNAN HANYOYIN SADARWAR👇🏽👇🏽_

*WHATSAPP*
 +2347055883010

*FACEBOOK:*
https://www.facebook.com/groups/222507361428028/

*TELEGRAM:*
https://t.me/joinchat/OOh5_RUljMIixFLQgNCDyg
Post a Comment (0)