HUKUNCIN GAISHE DA MARA LAFIYA DA FALALARSA 01



_*⚖ZAUREN MARKAZUS SUNNAH⚖*_

HUKUNCIN GAISHE DA MARA LAFIYA DA FALALARSA
                    

                _*DARASI NA DAYA*_

_Da Sunan *Allah* Mai *Rahma* Mai *Jinqai*_

_Musulunci Yayi Kira Zuwa ga Kyawawan 'Dabi'u, Wadanda Sune Suka Kunshi Rayuwar Musulmi Gaba Dayanta. Nassoshi daga cikin Alqur'ani da Ingantattu Hadisai da Dama Sun Kwadaitar Game da Siffantuwa da Dabi'u Nagari, Sannan Kuma Sukayi Hani da Fadawa Cikin Munanan Al'amuranki._

_Hakika Gaishe da Mara Lafiya Yana Daga Cikin Abinda Ake Siffanta Mutum Dashi Game da Kyakkyawar Dabi'a. Wanda Ziyartar Mara Lafiya Abu ne dake Sakawa Mara Lafiya Natsuwa, ta Kuma Sassauta Masa Radadin da Yake Fama dashi, Saboda Hakane Zaka Samu Idan Mara Lafiya Ya Samu Sauki Yakan Nuna Farin Cikinsa da Jin Dadi Ga duk Wadanda Suka Ziyarceshi a Yayin Rashin Lafiyarsa._

        _*FALALAR GAISHE DA MARA LAFIYA*_

_Gaida Mara Lafiya Tanada Falala Mai Tarin Yawa, Wanda Nassoshi Ingantattu da Dama Suka Tabbatar Dasu. Daga Cikin Wadannan Falaloli Akwai:_

_*1. KASANTUWA TARE DA ALLAH MADAUKAKI:* Duk Wanda Ya Ziyarci Mara Lafiya da Zimmar Duba Yanayin Halin da Yake Ciki tare da Jajanta Masa, Zai Kasance Yana Tare da Ubangiji Madaukaki. Hadisi Ya Tabbata, *Manzon Allah (ﷺ)* Yana Cewa:_

*ﻋﻦ ﺃﺑﻲ ﻫﺮﻳﺮﺓ ﻗﺎﻝ : ﻗﺎﻝ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﷺ : ‏”ﺇﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﻳﻘﻮﻝ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﻘﻴﺎﻣﺔ : ﻳﺎ ﺍﺑﻦ ﺁﺩﻡ، ﻣﺮﺿﺖ ﻓﻠﻢ ﺗﻌﺪﻧﻲ، ﻗﺎﻝ: ﻳﺎ ﺭﺏ، ﻛﻴﻒ ﺃﻋﻮﺩﻙ ﻭﺃﻧﺖ ﺭﺏ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ؟ ﻗﺎﻝ : ﺃﻣﺎ ﻋﻠﻤﺖ ﺃﻥ ﻋﺒﺪﻱ ﻓﻼﻧًﺎ ﻣﺮﺽ ﻓﻠﻢ ﺗﻌﺪﻩ؟ ﺃﻣﺎ ﻋﻠﻤﺖ ﺃﻧﻚ ﻟﻮ ﻋﺪﺗﻪ ﻟﻮﺟﺪﺗﻨﻲ ﻋﻨﺪﻩ. ﻳﺎ ﺍﺑﻦ ﺁﺩﻡ ﺍﺳﺘﻄﻌﻤﺘﻚ ﻓﻠﻢ ﺗﻄﻌﻤﻨﻲ، ﻗﺎﻝ : ﻳﺎ ﺭﺏ، ﻛﻴﻒ ﺃﻃﻌﻤﻚ ﻭﺃﻧﺖ ﺭﺏ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ؟ ﻗﺎﻝ : ﺃﻣﺎ ﻋﻠﻤﺖ ﺃﻧﻪ ﺍﺳﺘﻄﻌﻤﻚ ﻋﺒﺪﻱ ﻓﻼﻥ ﻓﻠﻢ ﺗﻄﻌﻤﻪ، ﺃﻣﺎ ﻋﻠﻤﺖ ﺃﻧﻚ ﻟﻮ ﺃﻃﻌﻤﺘﻪ ﻟﻮﺟﺪﺕ ﺫﻟﻚ ﻋﻨﺪﻱ...........“*.
```{ﺭﻭﺍﻩ ﻣﺴﻠﻢ}``` 

_An Kar6o Daga *Abi-Hurairah (ra)* Yace: *Manzon Allah (ﷺ)* Yace: Lallai Allah Yana Cewa a Ranar Kiyama: *“Ya Kai Dan Adam Nayi Rashin Lafiya Bakazo Ka Gaishe Ni ba”*. Sai Yace Ya Ubangiji Ya Za'ayi Nazo Na Gaiaheka Bayan Kaine Ubangijin Halittu. Sai (Ubangiji) Yace: *“Shin Bakasan Bawana Wane Yayi Rashin Lafiya ba Kuma Bakaje Ka Gaisheshi ba? Shin Bakasan da Kaje Dubashi Zaka Sameni a Wurinsa ba?” “Ya Dan Adam Na Ciyar Dakai Baka Ciyar Dani ba”*. Sai Yace Ya Ubangiji Taya Zan Ciyar Dakai Bayan Kaine Ubangijin Halittu. Sai (Ubangiji) Yace: *“Shin Bakasan Bawana Wane ne Ya Ciyar Dakai Kuma Kai Baka Ciyar Dashi ba, Shin Bakasan da Ka Ciyar dashi Zaka Samu (Ladan Ciyarwar) a Wurina ba?.........”*._
```{Muslim Ya Ruwaitoshi}```

```Tambihi:```
_Lallai Jingina Rashin Lafiya Ga Allah da Ubangiji Yayi a Wannan Hadisin Baya Nufin Ubangiji Yana Yin Rashin Lafiya a Hakikanin Zance, Abinda Hakan Yake Nuni dashi Shine Daukakar Bawa da Kuma Kusanci da Yake Samu da Allah a Yayin Ziyartar Mara Lafiyan da Yayi._

_Cewa Kuma da Ubangiji Yayi *(Zaka Sameni a Wurinsa)* Yana Nufin Zaka Samu Sakamako da Lada da Kuma Karamci a Wurin Wannan Mara Lafiyar daka Ziyarta._


_*YA ALLAH KA AZURTAMU DA LAFIYA KA KUMA BAMU IKON BAUTA MAKA DA LAFIYAR DA KA BAMU*_

_*✍🏼Abu-Aysha Al-Maliky*_

_ZAKU IYA BIBIYAR MU TA WAƊANNAN HANYOYIN SADARWAR👇🏽👇🏽_

*WHATSAPP*
 +2347055883010

*FACEBOOK:*
https://www.facebook.com/groups/222507361428028/

*TELEGRAM:*
https://t.me/joinchat/OOh5_RUljMIixFLQgNCDyg
Post a Comment (0)