ME YAKAMATA IN DINGA YI DOMIN IN NISANTA KAINA DAGA AIKATA ZUNUBI



*_ASSALAMU ALAIKUM_*
=
=
AMSOSHIN TAMBAYOYINKU
         
*DAGA ZAUREN
*📗ADDINI DA RAYUWAR DAN ADAM GROUP📗*
08186761010 ** 09038090522
:
.
_Tambaya ta (388)_
....
.ME YAKAMATA IN DINGA YI DOMIN IN NISANTA KAINA DAGA AIKATA ZUNUBI

_me yakamata in dinga yi domin nisanta kaina daga aikata xunubi_
.
_
::
*_AMSA:-_*
_To matakin farko da zaki bi shine: Ki sanya tsoron Allah da ganin girmansa a cikin zuciyarki sama da dukkan komai hakan zai taimaka miki wajen tsayar da ayyuka wajibabbu waďanda idan kika kiyayesu Allah zai tsareki daga aukawa zunubai musamman manyan zunubai misali kamar kiyaye Sallah yana hana aikata ayyukan zunubi Kamar yadda Allah madaukakin sarki yace damu a cikin littafinsa mai tsarki cewa: *ka tsayar da sallah Lallai Sallah tana hana al'fasha da abin kyama,kuma lallai ambaton Allah yafi girma, kuma Allah yana sane da Abinda kuke aikatawa.* Sannan ki dage wajen Ambaton Allah ta hanyar rokonsa(yin zikiri) domin datar dake zuwa ga ayyukan da ya yadda dasu kamar yawaita karatun al'kurani azkhar na yau da kullum wadanda manzon Allah ﷺ ya koyar musamman na safiya da yamma d.s.s. Hakanan yawaita istigfari da kabbarbari da Hailala d.s.s. lallai ki lazimci Addu'oi ingantattu wadanda suka zo cikin alkurani da hadisai Domin neman dacewa misali kamar faďin:_
_*RABBANA ATINA FIDDUNYA HASANATAN WAFIL AKHIRATI HASANATAN WAQINA AZABANNAR.*_
_Ma'ana: Ya ubangijinmu ka bamu mai kyau a cikin duniya da mai a cikin lahira kuma la tsare mana azabar wuta._
_*YA MUQALLIBAL QULUB SABBIT QALBI ALA DINIKA*_
_Ma'ana: Ya mai jujjuya/caccanza zukata ka tabbatar da zuciyata akan Addininka._
_*ALLAHUMMA MUSARRIFAL QULUBI SARRIF QULUBANA ALA 'DA'ATIKA.*_
_Ma'ana: Ya Allah mai jujjuya/sarrafa zuciya, ka tabbatar da zuciyarmu akan ďa'a/biyayya gareka._
..
_Wallahu A'alam_

_ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ_
_idan Anga Gyara A Sanar Damu  👏_
=
_Na So Kun San Tarin Lada Da Albarka Da Ake Samu Ta Hanyar Yada Ilimi  Ko Wani Alkhairi_
=
*MIFTAHUL ILMI*

ZaKu iya Bibiyar Mu 
Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)