NEMAN TSARI
Neman tsari shine neman kariya da taimkon akan wani abu da ke tsoron zai cutar da kai,kafin abun ya faru.
Neman tsarin Allah shine neman tsarin Allah daga sharrin halittarsa da neman Allah ya baka kariya daga dukkan sharri baki daya,kafin abun ya faru ta hanyar karanta abinda Allah da manzonsa suka suka bayyana ana samun kariyar Allah ta hanyar fadarsa ko karantasa.
Neman tsari kala ukkune
1-Neman tsarin Allah ta hanyar karanta surorin ko ayoyin neman tsari kamar Falaqi da Nasi da ayatul kursiyyu ko dukkan ayoyin Alqurani mai girma,ko kuma karanta adduoin da suka tabbata daga Manzon Allah s.a.w na neman tsari.
Wannan shine neman tsari na ibada,wanda ya aikata hakan yana samun tsarin Allah cikin yardar Allah daga dukkan wani sharri baki daya,sannan Ibadane za'a rubuta masa ladar yin hakan.
Neman irin wannan tsarin awajan wanin Allah shirkane babba.
2-Neman tsarin a wajan mutum cikin abinda yake ikon bada tsarin kuma an nemi tsarin ne ga mutumin da zai iya bada tsarin kuma yana wajan da ke nemam tsarin,wannan halasne babu laifi.
Amma idan ka nemi tsarin mutum wanda yake da ikon badawa sai karoki wanda baya nan kilama ya mutu sai kake kiransa kana neman tsarinsa,to yin hakan shirkane domin neman tsarin da babu ikone acikinsa ne sai ga Allah shi kadai.
3-Neman tsarin wanin Allah acikin abinda babu mai ikon bada wannan tsarin sai Allah shi kadai,to neman wannan tsarin awajan wani ba Allah ba shirka ne,kamar neman tsarin aljannu da bokaye da malaman tsubbu cikin abinda basu da ikon bada tsari sai Allah shi kadai.
Yin hakan shikrka ne babba kuma yana fitar da mutum daga musulinci domin juya hakkin Allah ne na bauta zuwa ga wanin Allah.
Allah ne mafi sani.
Allah ya kare mana imanin mu ya kuma bamu kariya daga dukkan sharri baki daya.