✿┈┈•🍃💜🌸•┈┈✿
RAHAMAR ALLAH GA BAWA.
Sahabi Abi huraira Allah ya kara yarda dashi yana cewa; "Ranar kiyama Allah zai matso da wani bawa kusa dashi, sai yasa wani abu ya rufeshi kada sauran halittu na filin kiyama su ganshi, sai Allah ya mika masa littafinsa acikin wannan abun (aboye daga shi sai Ubangijinsa), sai Allah ya ce masa "ya kai dan Adam karanta littafinka" sai ya fara karantawa, ya bude wurin kyawawan ayyukansa yana karantawa, alokacin fuskarsa zatayi haske, zuciyarsa zata cika da farin ciki, sai Allah yace masa " Shin kãsan ya kai bawana? Sai ya ce Na'am ya Ubangiji, sai Allah ya ce "Na karbama wadannan ibadun". Atake alokacin sai ya fadi ya yi sujjada, sai Allah ya ce masa "daga kanka ka cigaba da karanta littafinka", idan ya cigaba sai ya iso inda aka rubuta munanan ayyukansa, idan ya fara karantawa sai fuskarsa tayi baki, tsoro ya cika masa zuciya, jikinsa ya fara bari (karkarwa) atake alokacin sai kunyar Ubangiji ta kamashi, kunyar da ba wanda yasan irinta sai shi, sai Allah ya ce masa "shin kãsan ya kai bawana?? Sai ya ce Na'am ya Ubangiji, sai Allah yace "Na gafarta maka" sai ya fadi yayi sujjada.
Su kuma mutane baza su ga komai ba sai sujjadarsa da yake yi, har sai wasunsuma su fara cewa "Wannan bawan Allah kam ya ji dadi bai taba sabawa Allah ba kwata kwata, alhali basu san abunda ya hadu dashi ba tsakaninsa da Ubangijinsa ba".
جامع العلوم والحكم ٤٥٣
#Zaurenfisabilillah
TELEGRAM:
https://t.me/Fisabilillaaah
FACEBOOK:
https://www.facebook.com/Fisabilillaaah/