WASIYYAR SAHABI ABDULLAHI BN MAS'UD (R. A) YA YIN MUTUWARSA



WASIYYAR SAHABI ABDULLAHI BN MAS'UD (R. A) YA YIN MUTUWARSA

*✍️Yusuf Lawal Yusuf*

Daga Imam Ash-Sha'abiy ya ce: ya yin da mutuwa ta zo wa Abdullahi bn Mas'ud (R.A), sai ya kira ɗansa, ya ce ya Abdurrahman bn Abdullahi bn Mas'ud! Lalle ni zan maka wasiyya da abubuwa guda biyar, ka riƙe su daga gareni a tsawon rayuwarka:

1. Ka ɗebe tsammaninka daga mutane; domin shi ne wadata mai daraja.
2. Kuma ka bar neman biyan buƙata daga wurin mutane, domin haka kiran talauci ne wanda zai manne maka tare da kai ko yaushe.
3. Kuma ka bar duk abin da sai ka bawa mutane uzuri, kuma kar kayi aiki da shi.
4. Idan za ka iya kuma ace kar wani yini ya zo maka face wannan yinin na yau yafi alkhairi a kan na jiya; to kayi
5. Kuma duk lokacin da za kayi sallah kayi sallah kamar ta bankawa, kamar ba za kayi wata sallah ba bayan ta.

*📚 كلمات على فراش الموت، للشيخ وحيد عبد السلام بالي حفظه الله تعالى.*

*Darussa:*
1. Muhimmancin dogaro da Allah, bayan mutum ya yi ƙoƙarinsa. 
2. Neman na kai don tserar da mutumci, saboda abin hannun mutane da wuya. 
3. Gaggawar aikin alkhairi a lokacin da mutum ya samu dama, domin bai da tabbacin zai ƙara wasu mintuna. 
4. Neman yardar mutane abu ne mai matuƙar wuya a rayuwa. 

*19th Dhul-Qa'adah, 1442A.H*
*▪️➡️30th June, 2021⬅️▪️*
Post a Comment (0)