AN GAFARTA MASA ABINDA YA GABATA NA ZUNUBANSA
Akwai aiyukan ibda da Annabi SAW ya bada labarin cewar sanadiyyar aikatasu ana kankarewa bawa zunubansa baki daya kamar,aikin hajji, azumi, sallah alwalada sauransu.
Yin wannan adduar bayan gama cin abinci yana sanyawa Allah ya gafarta maka zunubanka baki daya.
Daga Mu'az bn Anas R.A yana cewa:
"Manzon Allah SAW yace:
(Duk wanda yaci abinci sai yace:
_"الحـمد لله الـذي أطعمـني هـذا ورزقنيـه مـن غـير حـول مـني ولا قـوة"_
"ALHAMDULILLAHIL LAZI ADH'AMANY HAZA WARAZAQNIHI MIN GAIRI HAULIN MINNI WALA QUWWATIN" an gafarta masa abinda ya gabata na zunubansa).
@رواه أبـو داود والـترمذي وقـال حـديث حـسن.
✔الـعَلّامَـة ابْـنُ عُثَيْـمِينْ -رَحِـمَه الله
Yana cewa:
"مـن غـير حـول منـي ولا قـوة:
Ma'ana badan Allah Madaukakin sarki ba ya saukaka maka ba wannan abinci ba da baka sameshi ba...."
@شـرح ريـاض الـصالحين〘4/198〙
Allah ka gafarta mana dukkan zunuban mu baki daya.