BAMBANCI {25}



BAMBANCI {25}

GARAFUNI

Garafuni shi ma wani ganye ne mai wanda ya shahara a kasar Hausa da yarbawa da kuma wasu qabilun daban wajan amfani da shi domin yin maganin abubuwa da dama, daga cikin abinda ake amfani da garafuni shi ne wajan magance matsalar Sihiri da tsafin maita da kuma Kambun baka da sauransu. Yadda ake amfani da shi a wannan fannin shi ne ga kadan daga ciki kamar haka:

1- Ana shanya shi sai a daka shi tare da barkono a hada da ya'yan habbah, sai arika yiwa mai mar lafiiyar hayaki da su insha ALLAHu duk wata maita ko kambun baka da ya kama mutum zai rabu da shi. Kuma wannan hadin hayakin yana daya daga cikin hayakin da suka fi karfi wajan matsawa da takurawa hassada, sihiri, maita da kuma kambun baka.

2- Ana ciro garafuni sai a sanya shi a ruwan wanka ya jika sosai sai a yi wanka da shi, yin hakan ma yana taimakawa kwarai da gaske wajan magance kambun baka da maita.

ALBABUNAJ (BADO)

Ana hada garin shi da na qustul Hindi da kuma jar kanwa (yar kadan) da ganyen shayin na'a na'a sai a tafasa su sai a zuba zuma a rika sha safe da daddare, wannan hadin yana magance matsalar ciwon mara mara misali irin wanda jinnu ke sanyawa kuma wannan hadin yana taimakawa wajan magance cutar (PID) da izinin ALLAH.

SANAMAKEEY (TAFASA)

Sanamakeey wacce da hausa muke ce mata tafasa, tana dauke da amfani mayawaita wajan rusa sihiri da lalata shi cikin iko da yardar Allah.

Yawancinmu sai dai mu ci ta ita kadai ko a kwadanta ta, da yawanmu bamusan amfaninta ba wajan warware sihiri, Insha ALLAHu a rubutu nagaba za mu fadi wasu daga cikin amfaninta wajan magance sihiri da Kuma yadda ake amfani da ita.
Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani. 

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu'ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu.🤲🏻)

Domin karin bayani:
👇👇👇

Dan uwanku:
Idris M Rismawy (Abu Nu'aym)

Gmail:
rismawy86@gmail.com

WhatsApp :
+2348031542026

Telegram Channel:
https://t.me/Rismawymedicine
Post a Comment (0)