HUKUNCIN ZUBAR DA CIKI (juna biyu)
*TAMBAYA*❓
Assalamu Alaikum malam jinjina, fatan alkhairi da kuma addu'ar cikawa da imani su tabbata agareka tare da iyalanka, iyaye, malumanka da kuma daliban wannan zaure mai albarka.
Malam tambayoyi nake dasu kamar haka.
Menene hukuncin matar da tazubda ciki (juna biyu)kuma shin zatayi kaffara kamar wanda yayi kisan kai? Kuma idan mijinta yasani kokuma sun hada kai tare wajen zubda cikin shima zaiyi kaffara?
*AMSA*👇
Wa alaikumus salam wa rahmatullah wa barakatuh.
Zubar da ciki don tsoron talauci yana daga cikin manyan zunubai domin shima kisan kai ne. In dai cikin yakai wata hudu zuwa sama.
Idan cikin yakai wata hudu to sannan an riga an busa masa rai. Idan mace ta zubar dashi da gangan, sai ta biya diyyah zuwa ga Waliyyan jaririn (wato dangin Ubansa).
Diyyar jariri shine kwatankwacin Rakuma guda biyar. Wato Ushurin diyyar Mace kenan. Kuma bayan haka zata 'yantar da Kuyanga guda, idan battta da kuyangar sai tayi azumi Sittin amatsayin kaffara.
Eh da Mijinta da duk wanda suke da hannu cikin kashe jaririn duk zasu hadu su biya diyyar. Kuma kowannensu sai ya 'Yanta Kunyanga ko kuma yayi azumi Sittin. Hujjah anan ita ce Hadisin nan na 6910 acikin Sahihul Bukhariy, kuma na 1681 acikin Sahihu Muslim. Duk sun ruwaito Hukuncin da Manzon Allah (saww) ya yanke ma matar data kwada ma wata Mai juna biyu dutse wanda yayi sanadiyyar mutuwarta da kuma jaririnta.
Amma idan cikin bai kai wata hudu da samuwa ba, To babu diyya ko kaffara amma duk da haka dai Zunubi ne mai girma. Don Qarin bayani aduba cikin MATALIBU ULIN NUHAA (juzu'i na 6 shafi na 50).
Wallahu A'alamu
Ku kasance damu domin ilimintarwa da Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177