SHIN WANI NA IYA YI MA WANI ISTIHARA?



SHIN WANI NA IYA YI MA WANI ISTIHARA?

*TAMBAYA*❓

Assalamou Alaikum wa Rahmatullah! Allah ya gafarta Malam ina da tambaya: shin mene hukuntchin Istiharar da Mutun yake zuwa wajen malami a kan wani abu da yake so ya yi ko neman zabi, sai malamin ya fada cewa akwai alkhairi ko kuma babu?

*AMSA*👇

Wa'alaikumus Salám, Istikhara na nufin neman zaɓin Allah a kan abin da mutum yake nema ko yake so. Istikhara a Musulunci ita ce mutum ya nemi zaɓin Allah a kan abinda yake nema ko yake so ta hanyar yin sallar Istikhara raka'o'i guda biyu, tare da yin addu'ar da Manzon Allah ﷺ ya koyar ta Istikhara, kamar yadda ya inganta a hadisi.

 Sahabin Manzon Allah ï·º Jabir É—an Abdullah ya ruwaito cewa Manzon Allah ï·º ya kasance yana koyar da su istihara a kan dukkan al'amura kamar yadda yake koya masu Sura a Alqur'ani, kamar yadda Imamul Bukhariy ya ruwaito a hadisi mai lamba ta 6382.

Sai wannan ya nuna cewa kowa ana so ne ya yi istikhara da kansa ba wai waninsa ya yi masa ba, saboda inda a ce wani na iya yi ma wani, istikhara da Manzon Allah ï·º ne ya fi cancanta ya yi wa Sahabbansa, tare da haka sai ba a ruwaito cewa yana yi masu ba, sai aka ruwaito cewa yana koya masu ne.

Kenan Æ´ar uwa babu maganar cewa mutum ya je wurin wani malami ya yi masa istikhara don ya gano masa shin abu kaza alheri ne ko ba alheri ne ba, yin wannan ba shi ake kira istikhara ba, wannan nau'i ne na Bokanci ko Tsubbu, saboda haka haramun ne zuwa yin wannan ko da mai yi É—in bai ce Tsubbu yake yi ba, saboda ba wanda ya san cewa abu kaza zai zama alheri ko ba zai zama ba sai Allah Subhaanahu Wata'ala.

Allah S.W.T ne mafi sani.

Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

Ku kasance damu domin ilimintarwa da Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Post a Comment (0)