IDAN ZAKAYI ADDU'A TO KAFARA ROƘAMA KANKA SANNAN KA ROƘAMA WANINKA
Yana cikin Ladubban addu'a wanda,mai addu'a ya fara da roƙama kansa sannan ya roƙama wanda yake so daga cikin mutane,wannan Shine Ladabin yin addu'a da Annabawa suke da salihan bayi kamar yadda Alƙur'ni ya bamu labari.
الشّيـخ محمّـد بن صالح العثيمــين -رحمـــه الله- :
Yace:-
*babban ladabi ga mai yin addu'a Shine ya fara yin addu'a ga kansa, sannan ya roqama waninsa, wannan shine Ladabin addu'a na Annabawa*.
Allah yana bamu labari game da addu'ar Annabwansa:-
Annabi Musa A.S yana cewa
▪*{ رب اغفر لي وﻷخي }*
_(Ya Allah ka Gafarta min kuma ka gafartama ɗan'uwana)_
Annabi Nuhu A.S yana cewa
*{ ربنا اغفر لي ولوالدي }*
_(Ya Ubangijin mu ka gafarta min kuma ka gafartawa mahaifana)_
Sai ya fara yin addu'a ga kansa sannan ya roƙawa mahaifansa.
Manzon Allah ﷺ ya yi Umarni ga Mai yin addu'a ya fara ga kansa sannan ka roƙama waninsa,Manzon Allah ﷺ yana cewa:-
*(Ka fara yin addu'a ga kanka)*ka fara yin addu'a ga kanka sannan ka roqama waninka shine yafi kyakkyawan ladabi ga mai yin addu'a.
@مــن شــرح ألفيّـــة ابـن مــــالك ( جـ1 \ صـ43 )
YIWA ƊAN UWNKA ADDU'A A BAYAN IDONSA
Allah yana cewa
*{والَّذِينَ جَاءوا مِنْ بَعْدِهِمْ يَقُولُونَ رَبَّنَا اغْفِرْ لَنَا ولإخْوَانِنَا الَّذِينَ سَبَقُونَا بالإيمَانِ}*
@الحشر: 10
Lokacin da Allah ya ambaci magabata na kwarai daga Muhajiran da Ansar, sai Allah ya kuma yabi wanda suka biyo bayan su da kyautatawa saboda addu'ar da suke yima magabata a bayan idonsu.
Allah yana Umanin Manzon Allah SAW ya yawaita nemawa kansa gafara, kuma ya nemawa muminai maza da mata gafara,sai yace
*{واسْتَغْفِرْ لِذنْبِكَ وَلِلْمُؤمِنِينَ والمؤْمِنَاتِ}*
@محمد: 19
Allah ya umurci Manzon Allah SAW da Al'ummarsa da su nemawa kansu gafara da sauran masu imani wanda ya hada wanda suke nan da wanda basu nan.
Manzon Allah ﷺ yana cewa:-
*(Babu wani bawa musulmi da zaiyi wa ƊAN UWANSA addu'a a bayan idonsa face MALA'IKA yace Allah ya amsa kuma kaima kana da irin abinda ka roƙa masa)*
@📜رواه مسلم.
Yazo a cikin Hadisi cewa:-
_Mafi alkhairi addu'ar musulmi itace wadda yayi wa ƊAN UWANSA a bayan idonsa kuma shima yana samun irin abin da ya roƙamasa, kuma addu'arsa karbabbiyace, kuma wasu daga cikin magabata sun kasance idan suna son wani abu a wajen Allah sai su roƙawa ƊAN UWANSA irin abin da yake so_.
Allah ne mafi sani