YABAR MATAR SA DA YA'YANSA SUNA YAWO DA GYALE



YABAR MATAR SA DA YA'YANSA SUNA YAWO DA GYALE

*TAMBAYA*❓

Assalamu alaikum wa rahmatullah ina ma mallam fatan alheri, mallam Tambaya kamar aka, ya dace magidanci ya bar matansa da ya'yansa suna yawo da gyele.
Mallam shin bashi da laifi idan ya kasance shi ya kokarin bin sunna aman su bai hana su saka gyale ba sobada ba a koda yaushe suke fita da gyale ba shin hakan ya dace jazakumullahu khair


 *AMSA*👇

Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuh. Alhamdu lillahi rabbil alamin wassalatu wassalamu ala rasulillah wa ala alihi wa sahbihi ajma'in.

Gaskiya bai dace ga magidanci ya zamo kan shiriya, sunnah, amma iyalin sa da yaran sa a kan bidi'a da saɓon Allah, domin amana ne Allah ya damƙa a hannun sa kuma yace ya kula da su ya tseratar da su daga wuta. Ba an ce yayi ta kan sa bane shi kaɗai, bar saura ko oho. 

(یَـٰۤأَیُّهَا ٱلَّذِینَ ءَامَنُوا۟ قُوۤا۟ أَنفُسَكُمۡ وَأَهۡلِیكُمۡ نَارࣰا وَقُودُهَا ٱلنَّاسُ وَٱلۡحِجَارَةُ عَلَیۡهَا مَلَـٰۤىِٕكَةٌ غِلَاظࣱ شِدَادࣱ لَّا یَعۡصُونَ ٱللَّهَ مَاۤ أَمَرَهُمۡ وَیَفۡعَلُونَ مَا یُؤۡمَرُونَ)
[Surah At-Tahrim 6]

Ya sani cewa gobe ƙiyamah ba zai kuɓuta a gaban Allah ba, sai yayi bayani kan amanar da aka bashi. Allah yace mu umarce iyalan mu da suyi sallah, Annabi yace a duke su idan ba suyi sallah ba a shekara goma. Allah yace 

(وَأۡمُرۡ أَهۡلَكَ بِٱلصَّلَوٰةِ وَٱصۡطَبِرۡ عَلَیۡهَاۖ لَا نَسۡـَٔلُكَ رِزۡقࣰاۖ نَّحۡنُ نَرۡزُقُكَۗ وَٱلۡعَـٰقِبَةُ لِلتَّقۡوَىٰ)
[Surah Ta-Ha 132]

Annabi sallallahu alaihi wa sallama yace 

5866 - «مروا أبا بكر فليصل بالناس» .
(صحيح) [حم ق ت هـ] عن عائشة ... [ق] عن أبي موسى ... [خ] عن ابن عمر ... [هـ] عن ابن عباس وسالم بن عبيد. فقه السيرة 499، الإرواء 541.

Bayan haka, Annabi yace mai rashin kishin iyali, yara mata, ko ƴan uwa mata, ba zai shiga aljanna ba, Annabi yace mutane uku ba su shiga aljanna, mai saɓa ma iyaye, daiyus da macen dake kama da maza

3063 - «ثلاثة لا يدخلون الجنة: العاق لوالديه والديوث ورجلة النساء» .
(صحيح) ... [ك هب] عن ابن عمر. حجاب المرأة المسلمة ص 67: حم، الضياء.

A nan nake so na jawo hankalin mata musulmi, su gane cewa, hijabi, addini ne, ibadah ce, Allah ne ya umarce su da shi. Allah ya fara da Annabi ne sannan aka zo ga sauran muminai, Allah yace

(یَـٰۤأَیُّهَا ٱلنَّبِیُّ قُل لِّأَزۡوَ ٰ⁠جِكَ وَبَنَاتِكَ وَنِسَاۤءِ ٱلۡمُؤۡمِنِینَ یُدۡنِینَ عَلَیۡهِنَّ مِن جَلَـٰبِیبِهِنَّۚ ذَ ٰ⁠لِكَ أَدۡنَىٰۤ أَن یُعۡرَفۡنَ فَلَا یُؤۡذَیۡنَۗ وَكَانَ ٱللَّهُ غَفُورࣰا رَّحِیمࣰا)
[Surah Al-Ahzab 59]

Daga ƙarshe saka gyale ba laifi bane idan zai rufe dukkan jiki, yana da kauri, babu ado, bai kama da na kafirai ba, ba mai ɗaukar ido ba, ma'ana dai idan ya cika sharuɗɗan hijabi.

Wallahu ta'aala a'lam.

 *_Amsawa_* :

 *Malam Aliyu Abubakar Masanawa*

Ku kasance damu domin ilimintarwa da Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Post a Comment (0)