Ramadaniyyat 1442H [22]
Dr. Muhd Sani Umar (Hafizahullah)
Sahabban Annabi (ﷺ) Kakaf Ba Munafuki (2)
__________________________
Ayoyin Alkur'ani cike suke da yabon sahabbai da bayanin falalarsu da yi musu shaida da imani da tsoron Allah. Ayar karshe da ta sauka a kan haka ita ce, ayar cikin [Suratut Tauba, aya ta 117-118].
Acikinta Allah (SWT) ya bayyana cewa, ya karbi tuban masu hijira, wadanda suka hada da na farko da na karshensu, da kuma mutanen Madina da wadanda ba na Madina ba.
Babu wani daga cikin mutanen da ke zaune a birnin Madina wanda bai je yakin Tabuka ba, sai wanda yake gajiyayye ne da wanda aka ba shi umarnin ya zauna tare da cewa shi ma yana tsananin kwadayin ya halarta. [Duba Bukhari #4423, Muslim#1911].
Don haka kowa ya fita ba wanda ya rage sai munafukai 'yan tsirari, kamar yadda hadisin Ka'ab dan Malik wanda yana daya daga cikin mutane uku da aka jinkirta karbar tubarsu saboda rashin fita yakin Tabuka. Inda yake cewa: "Na kasance duk sanda na fita na zagaya garin Madina ba wanda nake cin karo da shi sai mutumin da ake zargin sa da munafurci ko wanda Allah ya yi wa uzuri daga cikin masu rauni, wannan ya bakanta mini rai ainun". [Duba Bukhari#4418].
Wannan yana nuna cewa, an san ko su wane ne munafukai a dunkule, tun ma kafin a fita yakin Tabuka, sannan aka kara tabbatar da munafurcinsu bayan yakin Tabuka, saboda rashin fitarsu tare da Annabi (ﷺ) da rashin tubansu. Sannan Suratu Bara'a ta sauka ta kara falla su da tsiraita su.
Annabi (ﷺ) bai bar duniya ba, har sai da aka san su wane ne munafukai, ko dai ta hanyar yakini ko ta hanyar kakkarfan zato ko kuma ta hanya zargi.
Abin da yake kara nuna rashin yawansu da kuma kaskancinsu da tsanar da mutane suke nuna musu, shi ne rashin jin duriyarsu lokacin wafatin Manzon Allah (ﷺ).
To wadanda suke cikin irin wannan kunci, ba su da wani katabus na su rika ruwaito wani hadisi daga Annabi (ﷺ) har su karantar da mutane, domin duk wanda ya yi haka daga cikinsu ya san cewa, zai je fa kansa ne a cikin karin tuhuma da zargi, ko ma ya jawo wa kansa wani abin ki.
Malaman Sira sun ambaci sunayen wasu daga cikin munafukai, amma ba ko daya daga cikinsu da aka samu ya ruwaito wani hadisi daga Annabi (ﷺ). Duk wadanda suka yi ruwaya daga Annabi (ﷺ) sahabbai ne zababbu kuma sanannu babu munafiki ko daya daga cikinsu.
Walhamdulillah
https://t.me/miftahul_ilmi